Majiyoyi: Dalilin da yasa maharan jirgin kasan Kaduna suka farmaki magarkamar Kuje

Majiyoyi: Dalilin da yasa maharan jirgin kasan Kaduna suka farmaki magarkamar Kuje

  • A daren ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga suka kai wa gidan gyara halin Kuje ta Abuja hari da bama-bamai
  • Kamar yadda majiyoyi suka bayyana yan ta'addan da suka farmaki jirgin kasan Abuja-Kaduna sune suka kaddamar da harin saboda gwamnati tarayya ta ki saduda ta biya masu bukatunsu
  • Tun farko dai yan ta'addan sun nemi a sako masu mutanensu da ke kurkukun a madadin fasinjojin jirgin kasa da suka sace

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Yan bindigar da suka farmaki jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris ne suka kai hari gidan yarin Kuje a ranar Talata domin su kubutar da mambobinsu, kamar yadda wasu majiyoyi abun dogaro suka sanar da Daily Trust.

Daya daga cikin majiyoyin ta ce yan ta’addan sun farmaki gidan gyara halin sannan suka saki manyan mambobinsu saboda shirinsu na amfani da fasinjojin da suka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna wajen karbo mambobinsu bai yi tasiri ba saboda gwamnatin tarayya ta ki saduda.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hadimin Sheikh Ahmad Gumi ya fallasa sunan waɗan da suka kai kazamin hari gidan Yarin Kuje

Ya ce an yi amfani da abubuwan fashewa wajen fasa cibiyar gyara hali ta Kuje wanda hakan ya basu damar shiga cikin sauki.

Buhari a kurkukun Kuje
Majiyoyi: Dalilin da yasa maharan jirgin kasan Kaduna suka farmaki magarkamar Kuje Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Majiyar ta ce kari a kan bukatarsu na neman gwamnatin tarayya ta saki yaransu a madadin fasinjojin jirgin kasa da ke hannunsu, yan ta’addan masu biyayya ga bangaren ISWAP sun kuma nemi a saki wasu yan ta’adda da ke Kuje da wasu gidajen yarin,

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

“Sun gano cewa bukatarsu ba za ta biya ba don haka sai suka shirya ma yaki gadan-gadan.”

Ya ce suna kuma shirin kai farmaki ga runduna ta musamman da ke yaki da fashi da makami a Abuja wanda suka kaiwa hari a 2012.

An yi watsi da bayanan sirri

Wata majiya ta ce manya sun yi watsi da muhimman bayanan sirri da hukumomi masu alaka suka gabatar, lamarin da ya ba yan ta’addan damar shiga kurkukun Kuje cikin sauki da misalin karfe 10:30 na dare.

Kara karanta wannan

Harin gidan yarin Kuje: Atiku ya yi martani, ya bayyana babban damuwarsa kan lamarin

Ya ce baya ga masu gadin gidan yarin, akwai rundunar tsaro da suka hada da sojoji, yan sanda, SSS da civil defence da ke tsaron wajen saboda a nan ne aka ajiye manyan masu laifi.

“Abun bakin ciki akwai bara gurbi a koina don haka, duk da cewar an sanar da jami’an tsaro, yan ta’addan sun samu dama.
“Kuma wannan ne dalilin da yasa suka aiwatar da ta’assar daidai. Wasun su sun janye hankalin jami’an tsaro ta hanyar dana abubuwan fashewa da dama a wajen cibiyar bayan sun lalata ainahin kofar shiga, wanda ya baiwa wata kungiya daban da ke da alhakin fitar da mambobinsu dama ba tare da tangarda ba.
“Wadanda suka samu damar shiga sun tafi ne kai tsaye zuwa kurkukun da yan Boko Haram ke garkame sannan suka kubutar da su…Ba a samu wani turjiya ba.”

Rahoton ya kuma kawo cewa maharan sun yi amfani da nakiya sannan suka lalata cibiyar wacce ke cike da tsaro ciki harda babban sashin ta’addanci, inda suka saki dukkanin yan ta’addan da ke wajen.

Kara karanta wannan

Yanzu yanzu Abba kyari bai tsere ba inji hukumar NCoS

Majiyar ta ce:

“Ko shakka babu wadanda aka kubutar za su kawo cikas ga tsarin tsaron Najeriya; za su tayar da zaune tsaye har sai dai idan an yi wani abun.
“Kuma kamar yadda kuke gani, ba a kutsa sashin manyan mutane ba saboda wadanda aka tsare a wurin ba kansu aka yi shirin ba.”

Wata majiya ta ce:

“Da gangan aka kai harin daren saboda sun san cewa ba mu da karfin hana farmaki da daddare.
"Sun ceci mambobinsu cikin dare sannan kuma suka bace.”

'Yan ISWAP sun fitar da bidiyo, sun ce su suka kai farmaki magarkamar Kuje

Mun ji cewa Kungiyar ‘yan ta’addan SWAP ta dauki alhakin harin da aka kai gidan yarin Kuje da ke Abuja, rahoton Daily Trust.

Rahotanni a baya sun bayyana yadda ‘yan ta’adda suka kutsa cikin gidan yarin, a daren ranar Talata, inda suka saki fursunoni sama da 800, ciki har da manyan mutane da ke tsare a ciki.

Kara karanta wannan

Femi Falana ya Bukaci gwamnati tarayya da ta sauya fasalin tsaro a kasar

A wani faifan bidiyo da aka gani a daren Laraba, kungiyar ta'addancin ta nuna wasu daga cikin mutanenta suna harbi kan hanyarsu ta shiga cikin ginin magarkamar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel