Da Dumi-Dumi: Bayan farmakar Ayarin Buhari, Jirgin yaƙin Sojoji ya yi wa yan bindiga ruwan wuta a Katsina

Da Dumi-Dumi: Bayan farmakar Ayarin Buhari, Jirgin yaƙin Sojoji ya yi wa yan bindiga ruwan wuta a Katsina

  • Bayan harin da yan bindiga suka kai wa Ayarin shugaba Buhari, jirgin yaƙin NAF ya yi luguden wuta kan tawagar yan bindiga har biyu a Katsina
  • Bayanai da suka biyo bayan samamen na sama sun nuna cewa jirgin ya hallaka aƙalla yan ta'adda 42 a kauyukan ƙaramar hukumar Safana
  • Wannan na zuwa ne bayan yan ta'adda sun bindige mataimakin kwamishinan yan sanda a Dutsin-ma

Katsina - Wani samame ta sama da Jirgin yaƙin rundunar Operation Hadarin Daji ya gudanar ranar 5 ga watan Yuli, ya sheƙe yan ta'adda 42 a kusa da ƙauyukan Zakka da Umadan, ƙaramar hukumar Safana a Katsina.

A rahoton Leadership, wata majiya daga cikin jami'an tsaro ta ce jirgin NAF na tsaka da aikin sintiri, ya samu wasu bayanan sirri cewa anga gittawar wasu yan ta'adda tsakanin ƙauyukan Zakka da Umadan.

Kara karanta wannan

Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere

Bayanan sun fito ne bayan yan ta'addan sun farmaki ofishin yan sanda a ƙauyen Zakka biyo bayan cin ƙarfin dakarun yan sanda a Dutsin-ma, inda suka bindige kwamandan yankin har lahira.

Jirgin yaƙin NAF.
Da Dumi-Dumi: Bayan farmakar Ayarin Buhari, Jirgin yaƙin Sojoji ya yi wa yan bindiga ruwan wuta a Katsina Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Haka nan kuma a wannan rana ce, yan ta'addan suka farmaki Ayarin motocin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a kan hanyarsu ta zuwa Daura.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani Babban Jami'in Soja ya ce nan take jirgin NAF ya zarce zuwa wurin da aka ba shi bayani, bayan nazari da bincike ya gano inda yan ta'addan suke kilomila 7.1 daga yammacin garin Safana kuma yamma da ƙauyen Yartunda.

Ya ƙara da cewa binciken jirgin ya nuna masa wasu mazauna ƙauyen na yin takansu yayin da yan bindigan suka farmake su kuma suka shiga gida-gida suka sace wasu.

Ya cigaba da cewa:

"Jirgin ya bibiyi yan ta'addan har zuwa ginin da suka ɓoye mutanen da suka sato mai nisan kilomita ɗaya da sansanin su da suka tattaru, daga nan ne jirgin ya samu izinin sakin wuta."

Kara karanta wannan

Asiri ya Tonu: An kama manyan 'yan sanda biyu sun yi waya da yan ta'adda bayan harin gidan Yarin Kuje

"Bayan nasarar jirgin, mutanen ƙauyen da suka gudu lokacin da yan bindigan suka kai musu farmaki sun koma, haka nan waɗan da aka sace sun kuɓuta daga wurin da suke tsare."
"Mutanen ƙauye sun tabbatar da cewa harin jirgin saman, wanda ya gudana cikin natsuwa da kula, ya hallaka yan ta'adda 24."

Jirgin sama ya sake kai wa yan bindiga hari

Majiyar ta kara da cewa a wannan ƙaramar hukuma ta Safana, Jirgin NAF ya sake samun nasara kan yan ta'adda bayan samun bayanai da yammacin ranar 6 ga watan Yuli, 2022.

Bayanan sirrin sun bayyana cewa wasu yan ta'adda da garken shanu sun samu saɓani sun tarwatse daga sansanin wani ƙasurgumin ɗan bindiga, Abdulkareem, da ke kusa da ƙauyen Mahuta, a Safana.

"Nan take aka tashi jirgin yaƙi zuwa yankin, inda ya cigaba da jiran ko ta kwana zuwa safiyar 6 ga watan Yuli, lokacin da ya hangi yan ta'adda 18, ba da ɓata lokaci ba ya buɗe musu wuta."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe ‘ya’yan wani malamin addini a Adamawa, sun kuma yi awon gaba da diyarsa

Wani mazaunin garin Safana, Usman Mamman, ya shaida wa wakilin Legit.ng Hausa cewa suna fatan hakan ta faru amma abinda suka sani shi ne kuskuren sakar wa mutane Bam.

Ya tabbatar da cewa jirgin yaƙin sojojin Najeriya ya saki Bam kan mutane da ba su ji ba basu gani ba, ya jikkata da dama, ana cewa ma wasu sun mutu.

Haka nan wata mata data nemi a sakaya bayananta ts shaida wa wakilin mu cewa a gabanta aka kawo mutanen da uka jikkata a harin kuskuren sojoji.

Matar, wacce ta ce ta je babban Asibitin Dutsin-ma ne kasancewa mamarta bata da lafiya, ta ce wata mata ɗaya da rasu a gaban su, ta bar 'ya'ya da suka ji rauni.

A wani labarin kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa ya nesanta kansa da wani Hoto da aka ɗora shi kan daddumar Sallah

Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban kasa a 2023 ya nesanta kansa da Hoto da aka hangesa kan dardumar Sallah.

Kara karanta wannan

Jirgin Sojoji ya samu akasi, an yi wa Bayin Allah wuta ana zaune kalau a Katsina

Peter Obi ya ce Hotonsa da wasu suka ɗora kan sallayar Sallah ba dai-dai bane ko da kuwa sun yi da kyakkyawar niyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel