Hukumar Kula da Gidan kason Kuje tace an kwantar da kuran

Hukumar Kula da Gidan kason Kuje tace an kwantar da kuran

  • Hukumar Kula da Gidan Yari ta Najeriya (NCoS) ta ce zaman lafiya ya dawo gidan yarin kuje bayan harin yan bindiga a daren Talata
  • NCos ta fitar da wani jawabi akan fursunoni da ake zargi yan bindiga sun sako a harin ranar Talata
  • Ministan harkan cikin gida na Najeriya ya ce jami'an tsaro sun shawo kan lamarin babu dalilin ta da hankali

Brinin Abuja - Hukumar Kula da Gidan Yari ta Najeriya (NCoS), a ranar Laraba, ta ce zaman lafiya ya dawo a gidan kaso dake Kuje bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a daren ranar Talata. Rahoton Daily Trsut

A martanin da mai magana da yawun hukumar NCoS, Umar Abubakar ya mayar, ya tabbatar da cewa da misalin karfe 2200 na safe wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a tantance ko su wanene ba suka kai hari a gidan kaso dake Kuje a babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Dukkan kasurguman 'yan Boko Haram da ke daure a Kuje sun tsere, inji minista

kuje p
Tsaro : Hukumar Gidan yari tayi gum ‘Akan sakin fursunoni da akayi' FOTO : Premium Times

Sai dai hukumar ta NCoS ba ta tabbatar da ko an sako fursunoni ko ba a sako su ba a harin, amma majiyoyi sun shaida wa Daily Trsut cewa akwai wasu ‘yan ta’adda da maharan suka sako.

Ya ce jami’an rundunar ‘yan sandan NCoS da sauran jami’an tsaro da ke hedkwatar hukumar sun samu nasar dakile harin, inda ya kara da cewa “an samu kwanciyar hankali a wurin kuma sun shawo kan lamarin”.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake amsa tambayoyin, Kikiowo Ileowo, hadimin Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya ce: “Kada mu yanke hukunci tuktun. Sai dai abin da zan iya fada muku shi ne, ‘yan sanda, sojoji, jami’an Civil Dfense NSCDC, DSS suna nan a kasa kuma sun shawo kan lamarin. Babu dalilin ta da hankali kwata-kwata,"Inji.

A lokacin da ya kai wa wurin ziyara, Ministan Tsaro, Bashir Magashi, ya ce babu daya daga cikin wadanda ake zargi da laifin zama yan Boko Haram da suke tsare a gidan yarin Kuje da suka rage, duk sun tsere bayan harin daren ranar Talata.

Kara karanta wannan

Da dumidumi: Kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan yan Boko Haram sun farmakin gidan yarin Kuje – FG

Adadin wadanda aka kashe a Shiroro ya kai 48, ciki akwai Soji 34: Inji shugaban matasan yankin

Jihar Neja - Rahotanni da ke fitowa na nuna cewa an gano karin gawarwakin sojoji da jami’an ‘yan sanda da aka kashe a wani harin kwantan bauna da ‘yan ta’adda suka kai garin Shiroro na jihar Neja rahoton jaridar VANGUARD.

Wasu sun ta da zaune tsaye, sun kashe mai gadi, sun kone gidan mai a wata jiha Sani Kokki, shugaban matasan na jihar Neja, ya bayyana haka a ranar Lahadi, inda yace adadin wadanda suka mutu ya kai 48.

Asali: Legit.ng

Online view pixel