Gwamnatin tarayya ta zargi Boko Haram da kai mummunan hari Kuje Abuja

Gwamnatin tarayya ta zargi Boko Haram da kai mummunan hari Kuje Abuja

  • Gwamnatin tarayya ta zargi ƙungiyar Boko Haram da ɗaukar nauyin harin da aka kai gidan Yarin Kuje da ke Abuja
  • Ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ce duba da ɓarnar da akayi da dabarun harin, alamu sun nuna manufar da yan ta'addan suka je da ita
  • Yayin jawabinsa ga manema labarai bayan ziyarar wurin, Magashi ya ce a halin yanzu ƙura ta lafa, sojoji sun karɓi iko

Abuja - Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya zargi 'yan ta'addan Boko Haram da kai mummunan hari gidan yarin Kuje, dake birnin tarayya Abuja.

The Nation ta ruwaito cewa maharan sun farmaki gidan Yarin da misalin ƙarfe 10:25 na daren ranar Talata.

Ministan ya ce duba da kididdigar fursunonin da suka cika wandon su da iska da tsarin dabarun da aka bi wajen kai harin, duk alamu sun nuna manufar da ƴan ta'addan suka kudirta a zuciya.

Ministan tsaro, Bashir Magashi.
Gwamnatin tarayya ta zargi Boko Haram da kai mummunan hari Kuje Abuja Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Magashi yayin jawabi ga manema labarai kan harin Kuje, ya ce mambobin kungiyar Boko Haram 64 ne suka tsere daga Gidan Yarin bayan kai harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma ya ƙara da cewa a halin yanzun komai ya koma ƙarƙashin kulawa yayin da dakarun soji suka mamaye wurin kuma iko ya koma hannun su.

Ministan wanda ya kai ziyara gidan yarin tare da Hafsoshin tsaro ya ce:

"Muna iya bakin kokarin mu wajen ganin duk wanda ya tsere bai sha ba, mun dawo da su inda suke."

Ya ce jami'an tsaron da ke cikin harabar gidan Yarin sun yi kokarin maida martani iya karfin su amma yan ta'addan sun zo da adadi mai yawa na mayaƙa.

"Daga kididdigar da muka yi, suna da alaƙa da wata kungiya wato ƙungiyar ta'addancin Boko Haram, baki ɗaya mambobin su da ke ciki sun tsere."

"Amma yanzu komai ya dai-daita, shiyasa zaku ga mutane sun cigaba da harkokin su na yau da kullum. Mun nemi karin ɗauki kuma sojoji sun zo, sun karɓi ikon komai."

Ministan ya kara da tabbatar da cewa zuwa yanzu jami'ai sun samu nasarar sake damƙo waɗan da suka tsere kusan 200.

Yan bindiga sun far wa ayarin motocin shugaban kasa

A wani labarin kuma 'Yan bindiga farmaki jerin gwanon motocin shugaba Buhari a kan hanyar zuwa Daura a jihar Katsina

'Yan bindiga sun far wa tawagar motocin shugaban ƙasa Buhari a kan hanyar su ta zuwa Daura a shirye-shiryen zuwa Babbar Sallah.

Malam Garba Shehu, ya ce tawagar ta ƙunshi, hadimai, ma'aikata da yan jaridar gidan gwamnati amma Buhati baya ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel