Sarkin Gombe Ya Gana da Sarkin Zazzau, Sun Yi Magana kan Hadin Kai
- Sarkin Gombe, Abubakar Shehu Abubakar III ya kai ziyara fadar Sarkin Zazzau a Zaria don karfafa zumunci tsakanin masarautun biyu
- Sarakunan gargajiyan sun jaddada cewa hadin kan masarautu yana da muhimmanci wajen inganta zaman lafiya da ci gaban al'umma
- Sarkin Zazzau ya ce dangantakar masarautun Gombe da Zazzau ta koma zamanin jihadin Shehu Usman dan Fodio a karni na 19
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, ya kai ziyara ga Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, a fadarsa da ke Zaria, inda suka tattauna kan yadda za a karfafa haɗin gwiwar sarakunan gargajiya a fadin Najeriya.
A ziyarar da ya yi, Sarkin Gombe ya bayyana cewa ya zama wajibi sarakunan gargajiya su riƙa neman juna don tattauna batutuwan da suka shafi zaman lafiya da tsaro da kuma bunƙasa al'adu.

Source: Facebook
Abubakar A. Bello ya wallafa hotunan da Sarkin Gombe da tawarga shi suka dauka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dalilin zuwan sarkin Gombe Zaria
Sarkin Gombe ya ce manufar ziyarar ita ce ƙarfafa ƙawancen da ya wanzu tsakanin masarautar Gombe da ta Zazzau.
Ya kara da cewa ganawa tsakanin sarakuna na iya taimakawa wajen inganta tsaro, raya al'adun gargajiya, da kuma hada kan 'yan Najeriya.
Sarkin ya kuma yaba wa Sarkin Zazzau kan yadda yake gudanar da masarautarsa, yana mai cewa sarakunan gargajiya sun zama abokan hulɗa na gwamnati wajen kawo ci gaba mai ɗorewa da ƙarfafa zaman lafiya.
Bayanin da sarkin Zazzau ya yi
A nashi ɓangare, Sarkin Zazzau ya ce ziyarar ta nuna ƙarara cewa masarautun Najeriya na ci gaba da riƙe alaƙar da ta kasance a tsakaninsu, kuma duk biyu na da niyyar ɗaya wajen inganta haɗin kan ƙasa.
Ya ce dangantaka tsakanin masarautun Zazzau da Gombe tana da tarihin da ya fara tun karni na 19, wato a lokacin da Shehu Usman dan Fodio ya jagoranci juyin juya halin Musulunci wanda ya yaɗu a duk faɗin Arewacin Najeriya.
Sarkin Zazzau ya nuna cewa jagororin jihadin sun ƙarfafa ilimi, sun tsayar da mulki na gaskiya da zaman lafiya a yankunan su.
Ambasada Bamalli ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya baki ɗaya da su jkara hakuri da juna, yana mai cewa masarautu za su yi tsayuwar daka wajen tallafawa ilimi, raya al'umma da zaman lafiya a ƙasa baki ɗaya.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa ziyarar Sarkin Gombe zuwa Zaria ta jaddada muhimmancin masarautun gargajiya wajen magance ƙalubalen da ke fuskantar haɗin kan ƙasa.
Sultan ya gana da sarakuna
A wani labarin, mun kawo muku cewa mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar ya yi zama na musamman da sarakuna.
Taron ya hada manyan sarakunan gargajiya a Arewacin Najeriya da suka hada da Shehun Borno, Sarkin Zazzau da sauransu a jihar Kaduna.
Malamin addinin Musulunci da suka fito daga kungiyoyi daban-daban sun halarci taron domin tattauna matsalolin da suka addabi Arewa.
Asali: Legit.ng

