Nasara daga Allah: Sojoji da 'yan sa kai sun bindige 'yan ta'adda 8 a wata musayar wuta

Nasara daga Allah: Sojoji da 'yan sa kai sun bindige 'yan ta'adda 8 a wata musayar wuta

  • A kalla 'yan bindiga takwas sun ziyarci barzahu, yayin da suka yi yunkurin kai hari Anguwan Bashar da wata anguwa a karamar hukumar Kanam na jihar Plateau a ranar Litinin
  • An gano yadda sojin Najeriya da 'yan sa kai suka yi nasarar dakile harin 'yan ta'addan bayan mazauna yankin sun bayyana yadda suka umarcesu da su bar kauyukan ko su halakasu
  • Haka zalika, sanatan da ke wakiltar Plateau ta kudu, ya koka game matsalar rashin tsaro a wasu yankunan Kanam dake karamar hukumar Wase tare da bukatar agaji daga jami'an tsaro

Jos, Plateau - An ga a kalla gawawwaki takwas bayan 'yan bindiga sun kai hari Anguwan Bashar da wata anguwa a karamar hukumar Kanam na jihar Plateau a ranar Litinin.

Jami'in yada labaran soji na Operation Safe Haven na jihar Plateau, Manjo Ishaku Takwa, a ranar Talata, ya tabbatar da yadda 'yan bindiga suka kai hari anguwanni biyu ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan ta'adda sun halaka mataimakin kwamishinan 'yan sanda tare da jami'i 1

Kwamandan OPSH
Nasara daga Allah: Sojoji da 'yan sa kai sun bindige 'yan ta'adda 8 a wata musayar wuta. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Takwa ya labarta wa Punch a Jos yadda bayan hare-haren, wanda dakarun tare da hadin giiwar 'yan sa kai suka dakile harin, inda 'yan kauyen suka gano gawawwakin 'yan bindiga takwas.

Jami'in yada labaran sojin, wanda ya siffanta ragargazar da aka wa 'yan bindigan a anguwanni biyun a matsayin nasara, ya yi kira ga mazauna yankin da a koda yaushe su dinga sanarwa soji da sauran jami'an tsaro bayanan da suka dace lolaci bayan lokaci don su samu damar basu kariya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daya daga cikin 'yan sa kan da suka taimaka wajen samamen, Tasiu Ibrahim, ya ce kafin harin, 'yan bindiga sun sanarwa mazauna yankin cewa zasu kai musu farmaki.

A cewar Ibrahim, "Mun samu notis din zuwansu ranar Talatar da ta gabata, inda 'yan bindigan suka ce dole mu bar kauyenmu ko su halaka mu. Kuma mun gano yadda suka tura wa sauran kauyukan irin notis din.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan daba sun kai wa 'yan majalisa hari, sun raunata mutum 6, sun ragargaza motoci

"Bamu san idan za mu je ba, sanin kan kowa ne wadannan mutanen basa barazana a banza. Amma mun gode wa Ubangiji da basu yi nasara ba a lokacin da suka yi kokarin aiwatar da nufinsu a kan mu. Sai dai wasu daga cikinsu da suka rasa rayukansu saboda mun gano gawawwaki takwas bayan sun kawo mana farmaki."

Sanata mai wakiltar Plateau ta kudu, Farfesa Nora Daduut, ya koka game da rashin tsaro a wasu yankunan Kanam dake karamar hukumar Wase tare da kira ga jami'an tsaro da su kawo wa mutanen yankin agaji.

Na sadaukarwa da Najeriya rayuwata: Sojan da ya rasu a farmakin Shiroro

A wani labari na daban, daya daga cikin sojojin da 'yan bindiga suka halaka yayin harin mahakar ma'adanai tsakanin Ajata da Aboki a karamar hukumar Shiroro dake jihar Neja, a ranar Alhamis, ya ce ya sadaukar da rayuwarsa don tsare rayuwar 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun dakile harin yan bindiga a jahar Plateau

A wani bidiyo da aka wallafa a yanar gizo wasu watanni da suka shude kafin kai farmakin, sojan mai suna Hussaini Muhammadu daga jihar Jigawa ya bukaci 'yan Najeriya su yi addu'a ga dakarun da ke yaki a daji don tsare rayukan mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel