Da Duminsa: Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo, ya dira gidan yarin Kuje

Da Duminsa: Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo, ya dira gidan yarin Kuje

  • Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci gidan gyaan hali Kuje a ranar Laraba
  • Kamar yadda aka bayyana, ya sauka a jirgi mai saukar angulu wurin karfe 3:35 na yamma inda ya samu tarbar IGP
  • Ya kai ziyarar ne washegarin ranar da 'yan ta'adda suka kai mummunan farmaki gidan kurkukun inda suka saki masu laifi

FCT, Abuja - Bayan mummunan farmakin da 'yan ta'addan suka kai gidan gyaran halin Kuje dake Abuja, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci gidan kurkukun.

Sama da 'yan ta'adda dari ne suka tsinkayi gidan yarin a daren talata inda suka saki daruruwan mutane har da 'yan ta'addan dake garkame.

Labai da dumi
Da Duminsa: Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo, ya dira gidan yarin Kuje
Asali: Original

Vanguard ta ruwaito cewa, mataimakin shugaban kasan wanda ya sauka a jirgi mai saukar angulu wurin karfe 3:35 na yammacin Laraba, ya samu tarbar sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, IGP Usman Baba Alkali tare da sauran shugabannin tsao da manyan jami'an gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fallasa yan ta'addan da take zargi da kai hari Gidan Yarin Kuje

Karin bayani na nan tafe...

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Online view pixel