Yan ta'adda
Rundunar yan sandan jihar Enugu sun damke wasu manyan ‘yan ta’adda hudu da aka dade ana nema. An kama su da miyagun makamai da suka hada da bindigu da harsasai.
Wasu makasa da ake zargin na haya ne sun kai farmaki gidan ‘dan takarar majalisar jiha a Imo.Sun halaka shi tare da kone gidansa inda suka bar gawarsa a kasa.
Dubuwa wasu gawurtattun 'yan bindiga da aka dade ana nema a Katsina ta cika bayan yunkurin garkuwa da mutane da suka yi a kwatas din Sokoto-Rima a Katsina.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar ragargaza sansanonin 'yan bindiga a jihar.
A ranar Litinin da ta gabata, Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya kaddamar da yakin neman zarcewarsa. Buratai da Ali Modu Sheriff sun goyi bayansa.
Tsohon shugaban hukumar NERC ya bayyana damuwa bisa kin hukunta wadanda suka kashe dalibai FCE, Deborah Samuel da ta durawa Annabi SAW ashar a jihar Sokoto.
‘Yan sandan jihar Katsina sun dakile wani farmakin ‘yan bindiga a kauyen Unguwar Rinji dake karamar hukumar Kurfi. Sun ceto mutum biyar da aka yi garkuwa dasu.
An yi mummunan fada tsakanin ISWAP da Boko Haram, 'yan ta'addan Boko Haram sun tsere sun bar 'ya'yansu da matansu a maboyarsu, sun shiga hannun 'yan ISWAP.
Shahararren mai garkuwa da mutanen nan watao Dogo Gide yace sai an cika masa burins na biyan N100m akan dalibai da malamnan makarantar Yawuri ta jihar kebbi
Yan ta'adda
Samu kari