Rashin Tsaro: Gumi Ya Ragargaji Gwamnatin Najeriya Kan Barazanar Hukunta BBC Da Aminiya

Rashin Tsaro: Gumi Ya Ragargaji Gwamnatin Najeriya Kan Barazanar Hukunta BBC Da Aminiya

  • Sheikh Ahmad Gumi, malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna ya soki gwamnatin tarayya kan barazanar da ta yi na hukunta BBC da Aminiya
  • Gumi ya ce gwamnatin tana yunkurin rufe bakin kafafen watsa labarai ne kada su bayyanawa gazawarta wurin magance kallubalen tsaro a kasar
  • Malamin addinin musuluncin ya shawarci gwamnatin ta mayar da hankali wurin magance kallubalen tsaron da rashawa a bangaren tsaro duba da kudaden da aka kashe

Shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya soki gwamnatin tarayya kan barazanar da ta yi na hukunta kafafen watsa labarai game da wallafa rahotanni kan rashin tsaro da ya dade yana damun kasar, rahoton Channels TV.

A ranar Alhamis, Ministan Labarai da Al'addu, Lai Mohammed ya ce za a hukunta BBC da Trust TV saboda bidiyo da suka yi na yan bindiga.

Kara karanta wannan

Zulum: Fatara Da Talauci Na Iya Sa Wadanda Ke Sansanin Gudun Hijira Shiga Boko Haram

Sheikh Gumi Ya Soki FG Kan Barazanar Hukunta BBC Da Aminiya.
Rashin Tsaro: Gumi Ya Ragargaji Gwamnatin Najeriya Kan Barazanar Hukunta BBC Da Aminiya. Hoto: @ChannelsTV..
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma, a martaninsa, malamin addinin musuluncin ya ce gwamnati na kokarin rufe bakin kafafen watsa labarai su dena bayyana gazawarta da kawar da hankulan mutane daga rashawa na kashe kudi a bangaren tsaro.

Ya jinjinawa kafafen watsa labaran na gida da kasashen waje da suka nuna jarumta wurin wallafa rahoto kan tabarbarewar tsaro a yankin.

"Abin da ke faruwa a Najeriya yau musamman arewa maso yamma kamar yadda BBC ta rahoto yaki na kabilanci ne da ramuwar gayya saboda gazawar gwamnati ta magance rashin adalci da tun farko ake yi wa fulani," ya ce a lakcansa na mako-mako.
"Me ka ke tsammani daga al'umma (fulani) da aka bari cikin jahilci a lokacin da bata gari daga gwamnati da waje suka sace musu abin da rayuwarsu ta dogara a kai (shanu) ba kuma tare da an musu adalci ba.

Kara karanta wannan

Yadda Malamar Jami’a Ta Koma Tallan Dankali Saboda Yajin Aikin ASUU

"A yanzu da muke magana, ba a dena satar shanu ba. Hakan ya faru ga fulani da dama. Ina da hujjojin hakan wasu daga ciki ni da jami'an tsaro muka shiga tsakani. Ta yaya ka ke tsammanin gwamnati za ta magance rashin tsaro musamman wanda ya shafi fulani ba tare da magance batun kwace da satar shanu ba?"

Gumi ya ce abin tsoro yanzu shine Boko Haram ta fara shiga cikin fulani tana koyar da su akidarsu da manufarsu.

Ya shawarci gwamnati ta mayar da hankali kan yadda za ta magance matsalar a maimakon neman wanda za ta shafa wa laifi.

Gumi ya bukaci shugabannin hukumomin tsaro su tashi su yi aikinsu su.

NRC: Fulani Ba Yan Ta'adda Bane, In Ji Sheikh Ahmad Gumi

A wani rahoton, shugaban Kungiyar Kare Hakkin Makiyaya ta Nomadic Rights Concern (NRC), Farfesa Umar Labdo, ya ce fulani ba yan ta'adda bane, ko yan fashi ko bata gari, Nigerian Tribune ta rahoto.

A yayin taron manema labarai da ta kira a Kaduna a ranar Alhamis, yayin kaddamar da kungiyar, Labdo ta ce lokaci ya yi da yan Najeriya za su san cewa akwai bata gari a kowanne kabila. Don haka babu dalilin da zai sa a rika alakanta fulani da fashi ko ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel