El-Rufai: Buhari Bai Ma San Yan Ta'adda Sun Yi Barazanar Sace Shi Ba, Sai Da Na Sanar Da Shi

El-Rufai: Buhari Bai Ma San Yan Ta'adda Sun Yi Barazanar Sace Shi Ba, Sai Da Na Sanar Da Shi

Kaduna - Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ce shine ya fada wa Shugaba Muhammadu Buhari cewa yan ta'adda sun yi barazanar za su sace shi, rahoton Daily Trust.

A wani faifan bidiyo da aka saki a karshen mako, yan ta'ddan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja a watan Maris sun yi barazanar za su sace Buhari da El-Rufai.

Buhari da El-Rufai
El-Rufai: Buhari Bai Ma San Yan Ta'adda Sun Yi Barazanar Sace Shi Ba, Sai Da Na Sanar Da Shi. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Da ya ke magana a wani shirin rediyo da wakilin Daily Trust ya bibiya a daren ranar Lahadi, gwamnan yace shi kansa an masa gargadi ya rika takatsantsan da iyalansa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya yi bayanin cewa tun shekaru biyar da suka shude ya rika bada shawarar a yi wa yan ta'addan ruwan bama-bamai a duk inda suke, yana mai cewa wannan ne kawai mafita.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Buhari zai sanya takunkumi kan BBC da Aminiya saboda kambama 'yan ta'adda

"Na ma samu labarin bidiyon inda suka yi barazanar sace Buhari da ni. An gargade ni in rika taka tsantsan da iyalai na. Ta yaya za mu zauna a kasar da yan ta'adda za su rika yi wa Shugaban kasa barazana kuma akwai sojoji da yan sanda?
"Idan a baya wadanda ke gwamnati na ganin abin wasa ne kawai da ke shafar yan Katsina, Zamfara, Kaduna da Niger, yanzu abin ya zo gida kuma dole mu tashi mu yake shi. Shi yasa ya gana da shugaban kasa a ranar Lahadi na fada masa matsalolin. Na kuma fada masa batun bidiyon domin har zuwa ranar bai sani ba. Na fada masa kuma bayan kwana ɗaya gwamnan Zamfara ya sake tabbatar masa kuma shima ya ga bidiyon domin a dauki mataki.
"Shugaban kasa ya tabbatar min cewa ya zauna da shugabannin tsaro kwana 3 zuwa 4 kafin haduwar mu kuma ya bawa sojojin umurnin su magance abin. Muna fata, da izinin Allah sojoji da yan sanda da aka bawa umurnin za su gama aikin. Ba sai mun jira yan ta'addan sun kawo hari kafin mu mayar da martani ba," in ji El-Rufa'i.

Gwamnan na Kaduna ya ce sojojin su bi yan ta'addan duk inda suke su gama da su. Maganan gaskiya shine mun damu da matsalar tsaro kuma muna fata gwamnatin tarayya za ta dauki matakin da ya dace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel