Sokoto: Yadda Mutum 26 Suka Nutse A Ruwa Suka Mutu Sakamakon Gumurzu Da Yan Bindiga Da Jami'an Tsaro Suka Yi

Sokoto: Yadda Mutum 26 Suka Nutse A Ruwa Suka Mutu Sakamakon Gumurzu Da Yan Bindiga Da Jami'an Tsaro Suka Yi

  • An gano gawarwakin mutane 26 mazauna kauyen Duma da ke karamar hukumar Tureta a Jihar Sokoto da suka nutse a ruwa
  • Rahotanni sun bayyana cewa mutanen sun nutse ne sakamakon firgici a lokacin da jami'an tsaro ke musayar wuta da yan bindiga a wani daji da ke kusa da garin
  • Kakakin yan sandan Jihar Sokoto, DSP Sanusi Abubakar ya tabbatar da mutuwan mutanen 26 amma ya ce ba gaskiya bane wai yan sanda suka harbe su don babu alamar harbin bindiga a jikinsu

Jihar Sokoto - An gano gawarwaki a kalla guda 26 na mazauna kauyen Duma a karamar hukumar Tureta kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Rahotanni sun ce mutanen sun nutse ne a ruwa a yunkurin tserewa daga musayar wuta da ake yi tsakanin jami'an tsaro da yan bindiga a wani daji da ke kusa da su.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutum 6 A Katsina, Sun Nemi A Biya Kudin Fansa Miliyan N50

Taswirar Jihar Sokoto.
Sokoto: Yadda Mutum 26 Suka Nutse A Ruwa Sun Mutu Yayin Da Yan Bindiga Da Jami'an Tsaro Ke Musayar Wuta. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daily Trust ta gano cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba da ta gabata a yayinda jami'an tsaro na Operation Hadarin Daji suka yi gumurzu da wasu da ake zargin yan ta'adda ne da suka sace shanu a wasu garuruwan Jihar Zamfara da ke makwabtaka da Sokoto.

Kakakin yan sandan Sokoto, DSP Sanusi Abubakar, yayin tabbatar da lamarin yace yan kauyen sun ji karar harbin bindiga daga daji kuma suka hango wasu yan bindiga da aka fatattako, sun firgita sun fara guje-guje.

Ya ce:

"Sun yi tunanin yan bindigan da ke tserewar za su zo kawo musu hari ne. Suka fara guje-guje sakamakon hakan wasu suna nutse. Daga bisani an gano gawarwaki 26 an kuma birne su."

Abubakar ya ce har yanzu ana jami'an tsaro na hadin gwiwa suna cigaba da atisaye a yankin sun kuma zagaye wurin.

Kara karanta wannan

Harin Kwanton Bauna: Yan Bindiga Sun Afka Wa Tawagar Yan Sanda Sun Kashe Jami'i Daya

Yan sanda ba su harbi mutane ba, SP Abubakar

Amma, ya yi watsi da rahoton cewa yan sanda sun harbi wasu mazauna kauyen, yana mai cewa babu alamar harbin bindiga a jikin dukkan gawarwakin da aka gano.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a ranar Juma'a ya mika ta'aziyya ga mutanen kauyen kan afkuwar lamarin.

An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta

A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel