Borno: Sojoji sun sake ceto ‘yan mata 2 na makarantar Chibok da Boko Haram suka sace

Borno: Sojoji sun sake ceto ‘yan mata 2 na makarantar Chibok da Boko Haram suka sace

  • Rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar ceto wasu 'yan mata biyu daga cikin 'yan matan Chibok da aka sace
  • A baya an ceto wasu 'yan mata biyu daga cikin 'yan matan Chibok da ke hannun Boko Haram tsawon shekaru sama da takwas
  • Kungiyoyin ta'addanci a Najeriya sun sha sace dalibai, tun bayan da kungiyar ta fara sace 'yan mata sama da 100 a Borno

Bama, Borno - Akalla shekaru takwas bayan kai mummunan hari Chibok da kuma sace 'yan mata a wata makarantar sakadaren garin, rundunar soji ta kubutar da wasu daga cikin 'yan matan.

A rahoton da muka samo daga jaridar Leadership, an ce jami'an sun ceto biyu daga cikin 'yan matan sama da 200 da aka yi garkuwa dasu kuma aka yi musu auren dole tun shekarar 2014

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka farmaki motar kudi, suka hallaka ma'aikacin banki

Wani rahoton sirri daga manyan majiyoyin tsaro, sun tabbatar da ceto 'yan matan daga sansanin Gazuwa, wata hedikwatar kungiyar Boko Haram da aka fi sani da Gabchari, Mantari da Mallum Masari, mai tazarar kilomita tara zuwa garin Bama.

'Yan matan Chibok sun sake kubuta daga hannun Boko Haram
Borno: Har ila yau, Sojoji sun ceto ‘yan matan makarantar Chibok 2 | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Makwannin da suka gabata ne rundunar sojin Najeriya ta ceto wasu 'yan matan daban, kana suka ba da labarin cewa akwai sauran 'yan mata sama da 20 da ke hannun 'yan ta'addan har yanzu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

‘Yan matan makarantar ta Chibok biyu da sojoji suka ceto a baya kuma aka nuna su ga jama’a a kwanan baya su ne Mary Dauda da Hauwa Joseph.

Tserewar da suka yi daga sansanin ‘yan ta’addan ya faru ne, sakamakon gagarumin farmakin da dakarun Operation Hadin Kai suka ci gaba da yi wanda ya yi sanadin bullar yunwa da kauran dole a yankunan ‘yan ta’addan, inji Telegraph.

Kara karanta wannan

Fargabar kai hari fadar Buhari: IGP ya umarci a tsaurara matakan tsaro a Abuja

Idan za ku iya tunawa kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da dalibai mata 276, masu shekaru tsakanin 16 zuwa 18 a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a ranar 14 ga Afrilu, 2014.

Sama da ‘yan matan makarantar 100 ne har yanzu ba a gansu ba ya zuwa ranar 14 ga Afrilu, 2021, shekaru takwas bayan da ‘yan ta’addan suka sace su.

Daya daga cikin 'yan matan Chibok: Na san marigayi Shekau, sauran mata 20 a hannun BH

A wani labarin, shekaru takwas bayan da mayakan Boko Haram suka sace ‘yan mata 276 a makarantar Sakandaren Chibok a Borno, rundunar sojin Operation Hadin Kai ta ceto wasu karin ‘yan matan Chibok biyu a dajin Sambisa.

An ce rundunar ta ceto su ne a yankin Gazuwa da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno a kwanan baya. Wadanda aka kubutar din su ne Mariam Dauda da Hauwa Joseph ne tare da jariransu, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani rahoton sirri ya fallasa, 'yan ta'adda sun tara makamai za su afkawa jihar Buhari

Bayan ceto su sun ba da labarin wahalar da suka sha na tsawon shekaru takwas a cikin dajin a wani taron manema labarai da aka gudanar a babban dakin taro na Command-and-Control Center da ke Maimalari a Maiduguri ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel