Amurka Ta Kashe Ayman al-Zawahiri, Mutum na Biyu ga Osama Bin Laden

Amurka Ta Kashe Ayman al-Zawahiri, Mutum na Biyu ga Osama Bin Laden

  • Shugaba Joe Biden, ya bayyana cewa jiragen yakin Amurka sun kashe Ayman al-Zawahiri, Mutum na Biyu ga Osama Bin Laden a Afganistan
  • Biden ya ce jami’an leken asirin Amurka sun gano inda al-Zawahiri yake a cikin farkon wannan shekara a lokacin da ya kai wa iyalin sa ziyara
  • Al-Zawahiri wanda asali dan kasar Misira ne ya cigaba da jagorantar Al-Qaeda bayan mutuwar Osama bin Laden

Amurka - Shugaba Joe Biden, a jawabin da yayi wa manema labarai a yammacin jiya, ya ce umarnin kai hari da ya ba jiragen yakin Amurka a birnin Kabul na Kasar Afganistan yayi sanadiyar kashe al-Zawahiri.

Al-Zawahiri ya kasance jagora na farko ga tsohon shugaban Al-Qaeda, Osama bin Laden, wanda sojojin Amurka suka kashe a lokacin da yake buya a Pakistan a shekarar 2011.

Kara karanta wannan

Dan Kungiyar Asiri Ya Dana Wa Kansa Harsashi A Lokacin Da Ya Ke Kokarin Sarrafa Bindiga

Al-Zawahiri wanda asali dan kasar Misra ne ya cigaba da jagorantar Al-Qaeda bayan mutuwar Osama bin Laden.

Ayman
Amurka Ta Kashe Ayman al-Zawahiri, Mutum na Biyu ga Osama Bin Laden FOTO REUTERS
Asali: UGC

A cikin jawabin nasa, Biden ya ce al-Zawahiri na da hannu dumu-dumu a harin ranar 11 ga watan Satumba, 2001, wanda ya kashe kusan Amurkawa 3,000, da kuma kitsa harin bam na USS Cole a shekara ta 2000, wanda ya kashe Amurkawa 17 na ruwa tare da jikkata wasu da dama.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Biden ya ce tun lokacin da al-Zawahiri ya karbi ragamar kungiyar Al-Qaeda daga hannun bin Laden, ya cigaba da juya lamuran kungiyar a fadin duniya inda yake fitar da bidiyoyin kira ga kai hari kan Amurka da kawayenta.

Ya ce jami’an leken asirin Amurka sun gano al-Zawahiri a cikin garin Kabul a farkon wannan shekarar a lokacin da ya je kai wa iyalansa ziyara.

Kara karanta wannan

Elrufai Ya Ce APC ta Riga Ta Nada Darakata Janar Na Kamfen Din Takarar Tinubu Da Shettima

Biden ya ce:

"A yanzu haka anyi adalci kuma mutanen duniya su daina jin tsoro saboda wannan shugaban na yan ta’adda baya nan domin an kashe shi.

Sokoto: Yadda Mutum 26 Suka Nutse A Ruwa Suka Mutu Sakamakon Gumurzu Da Yan Bindiga Da Jami'an Tsaro Suka Yi

A wan labari kuma, An gano gawarwaki a kalla guda 26 na mazauna kauyen Duma a karamar hukumar Tureta kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Rahotanni sun ce mutanen sun nutse ne a ruwa a yunkurin tserewa daga musayar wuta da ake yi tsakanin jami'an tsaro da yan bindiga a wani daji da ke kusa da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel