Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kashe Kwamandan Yan Bijilanti a Jihar Yobe

Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kashe Kwamandan Yan Bijilanti a Jihar Yobe

  • Yan ta'addan ƙungiyar Boko Haram sun shiga har cikin gida, sun kashe kwamandan jami'an tsaron Sa'kai a jihar Yobe
  • Bayanai sunyi nuni cewa yan ta'adda sun shiga garin Buni Yadi kuma suka nufi gidan kwamandan kai tsaye suka kashe shi
  • Magajin Garin Shuwarin ya roki mutane su kai rahoton duk wani motsi da suke zargi ga jami'an tsaro

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Yobe - Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kashe kwamandan yan Bijilanti da aka fi sani da yan Sa'kai, Umaru Balami, a garin Buni Yadi, ƙaramar hukumar Gujba a jihar Yobe, arewa maso gabashin Najeriya.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa yan ta'addan sun kashe Balami ne a cikin gidansa ranar Talata.

Tasiwirar jihar Yobe.
Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kashe Kwamandan Yan Bijilanti a Jihar Yobe Hoto: punchng
Asali: UGC

Wani mazaunin yankin wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya ce yan ta'addan sun shiga gari ne a kan Babura kuma suka tafi kai tsaye zuwa gidan Kwamandan jami'an tsaron, wanda a lokacin aka ce yana kwance yana bacci.

Kara karanta wannan

An Yi Jana’izar Daya Daga Cikin Sojojin Da Yan Bindiga Suka Kashe A Abuja, Hotuna

Bayanai sun nuna cewa wadan da ke tsaron kwamandan sun yi yinkurin gwabza wa da maharan amma suka ci ƙarfin su saboda sun fi su muggan makamai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Magajin Garin Shuwarin, Lawam Gujja Abubakar, ya ce:

"Mun wayi gari da mummunan labari ranar Laraba da safe kasancewar mayaƙan Boko Haram sun kashe kwamandan yan Bijilanti, Umaru Balami, a gidansa."

Ya bayyana cewa an ɗakko gawar marigayi Kwamandan jami'an daga cikin gidansa cikin jini washe garin ranar da yan ta'addan suka kai masa hari.

Magajin Garin ya yi Addu'ar Allah ya kyautata makwancin marigayin, sannan ya yi kira ga mutanen garin da baki ɗaya yankin ƙaramar hukumar Gujba da su kai rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba ga hukumomin tsaro.

Halin da mazauna yankin ke ciki

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Litinin, mazauna yankin sun ga ayarin mayaƙan Boko Haram da motoci biyu da Mashina sun nufi yankin daga wajen gari da nufin ta da hankali.

Kara karanta wannan

Hotunan Yadda Dan Siyasar Kebbi Ya Zage Yana Taya Al’ummar Mazabarsa Sharan Kwata

Wata majiya mai ƙari ta tabbatar da cewa hukumomin soji sun haɗa tawaga kuma sun tura dakarun soji tare da Yan Sa'akai yankin don samar da tsaro, haka nan a Gujba.

A wani labarin kuma NSA Babagana Monguno ya ce tabarɓarewar tsaro ta mai yan Najeriya bango, sun fara fafutukar neman ɗaukin kare kai

Ya ce a yanzu haka gwamnatin ta duƙufa aiki da dare ba rana kan sabbin dabarun da zasu kawo ƙarshen matsalar tsaro baki ɗaya a Najeriya.

A cewarsa, majalisar koli ta tsaro ta amince da wasu sabbin dabaru domin ganin bayan matsalar, ya tabbatar da cewa za'a ƙara matsa kaimi kan ayyukan ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel