'Yan Afghanistan Sun Bayyana Shakku Kan Kashe Al-Zawahiri Na Al-Qaeda a Kabul

'Yan Afghanistan Sun Bayyana Shakku Kan Kashe Al-Zawahiri Na Al-Qaeda a Kabul

  • Da yawa daga cikin ‘yan Afghanistan sun bayyana shakku akan kashe shugaban Al-Qaeda da Amurka ta yi a Kabul
  • A Ranar Litinin ne Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewa jiragen yakin Amurka sun kashe Al-Zawahiri
  • Wasu yan kasar Afghanistan suna ganin labarin kashe alzwahiri Fargandar Amurka ce kawai inda suka bukaci a nuna musu shaida

Afganistan - Da yawa daga cikin ‘yan Afghanistan sun bayyana kaduwarsu ko kuma shakku a yau talata game da labarin kashe shugaban Al-Qaeda a Kabul sakamakon wani harin da jiragen yakin Amurka maras matuki suka kai musu, suna masu cewa ba za su yarda Ayman Al-Zawahiri ya boye a tsakiyarsu ba.

Fahim Shah, wani dattijo mai shekaru 66, mazaunin babban birnin Afghanistan, ya shaida wa AFP cewa Farfaganda ce kawai.

Kara karanta wannan

Ke duniya: A kan N50,000, matashi ya halaka kawar kanwarsa, ya birne gawarta a dakinsa

Sun fuskanci irin wannan farfagandar a baya kuma babu wani abu a ciki, a zahiri, baya tsammanin an kashe shi.

Zawahiri
'Yan Afghanistan Sun Bayyana Shakku Kan Kashe Al-Zawahiri Na Al-Qaeda a Kabul FOTO REUTERS
Asali: UGC

Wani mazaunin birnin Kabul, Abdul Kabir, ya ce yaji karar harin da safiyar Lahadi, amma duk da haka ya yi kira ga Amurka da ta tabbatar da wanda suka kashe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kabir ya ce, ya kamata su nunawa mutane da duniya cewa sun kashe mutumin nan kuma ga shaida.

Da yammacin jiya litinin ne, shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da kisan Zawahiri, inda ya ce "an yi adalci" ga dan kasar Masar da aka sanya la’adan miliyan 25 a kansa.

Wani babban jami'in Amurka ya ce dan shekaru 71 a duniya yana kan baranda na wani gida mai hawa uku a unguwar Sherpur aka kai masa hari da makami mai linzami guda biyu jim kadan bayan wayewar garin Lahadi.

Kara karanta wannan

Jiragen Yakin Amurka ya Kashe Ayman AlZawahri, Shugaban Al-Qa'ida

Kungiyar Taliban ta bayyana cewa a ranar Talata Amurka ta kai wani harin jirgi mara matuki, amma ba ta bayar da cikakken bayani kan wadanda suka mutu ba kuma ba ta bayyana sunan Zawahiri ba.

A ranar Lahadin da ta gabata ne ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta musanta rahotannin wani harin da jiragen yaki mara matuki suka kai, amma kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya fada jiya talata suna gudanar da bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel