Yan 'Boko Haram' Sun Kai Hari Hedkwatar Ƴan Sanda A Kano, Sun Yi Harbe-Harbe

Yan 'Boko Haram' Sun Kai Hari Hedkwatar Ƴan Sanda A Kano, Sun Yi Harbe-Harbe

  • Wasu yan ta'adda da ake zargin yan Boko Haram ne sun tafi hedkwatar yan sanda da ke Kano kan layin BUK road sun yi harbe-harbe
  • Majiyoyi daga hukumomin tsaro sun tabbatar da afkuwar harin da aka ce ya faru misalin karfe 12.30 na ranar Juma'a
  • Amma, hedkwatar rundunar yan sandan ta bakin kakakinta SP Abubakar Ambursa ta karya afkuwar lamarin tana mai cewa wasu ne kawai suka kirkiri labarin

Jihar Kano - Wasu da ake zargin yan Boko Haram ne sun harba bindiga a hedkwatar rundunar yan sandan Najeriya ta Zone 1 da ke BUK road a Kano, Daily Nigerian ta rahoto.

Ita ma jaridar Leadership ta rahoto cewa wata majiyar tsaro ta ce yan ta'addan sun zo a motocci guda uku misalin ƙarfe 12.30 na ranar Juma'a suka yi harbe-harbe sannan suka tsere.

Kara karanta wannan

Labari da duminsa: 'Yan daba sun farmaki coci, sun sace na'urorin buga katin zabe

Yan Sandan Najeriya.
Yan 'Boko Haram' Sun Kai Hari Hedkwatar Ƴan Sanda A Kano. Hoto: @LeadershipNGA.
Asali: UGC

Majiyar tsaron ta ce an tsaurara tsaro a kusa da hedkwatar yan sandan domin kare afkuwar yiwuwar hari daga yan ta'addan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idan za a iya tunawa, yan ta'addan sun kai hari hedkwatar yan sandan a ranar 20 ga watan Janairun 2012 inda wasu mutane da dama suka rasu.

Martanin Rundunar Yan Sanda

Duk da cewa manyan jami'an yan sanda uku sun tabbatarwa Daily Nigerian afkuwar lamarin, rundunar ya karyata rahoton, tana mai cewa ba a yi harbi a hedkwatan yan sanda ba.

Kakakin hedkwatan yan sanda, SP Abubakar Ambursa, ne ya karyata rahoton a lokacin da ya yi magana da manema labarai a Kano.

"An janyo hankalin mu kan wani rahoto da ke yawo na cewa yan ta'adda sun yi harbi a hedkwatar mu a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Abuja, Sunyi Awon Gaba Da Mutane a Gona

"Ba abu mai kaman haka da ya faru. Ba komai bane illa karya da wasu suka shirya.
"Akwai masallacin Juma'a kusa da hedkwatan, kuma a lokacin da suka ce yan ta'addan sun yi harbin, lokacin sallah ne, domin mun yi salla karfe 1 na rana," in ji Ambursa.

Amma, Daily Nigerian ba ta janye rahoton ta ba na cewa tabbasa an yi harbi a hedkwatar misalin karfe 12.30 na rana, lamarin da ya sa yan sanda suka rufe hanyar da za ta bulla zuwa hedkwatar aka kuma tsaurara matakan tsaro a birnin.

Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Abuja, Sunyi Awon Gaba Da Mutane a Gona

A wani rahoton, kun ji cewa an sake kai hari a karamar hukumar Kwali a Abuja yayin da lamarin tsaro ke cigaba da tabarbarewa a babban birnin tarayyar, Daily Trust ta rahoto.

A kalla sau uku yan bindiga suka kai hari a cikin makon nan a Abuja hakan yasa gwamnatin tarayya ta umurci a rufe FGC, Kwali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel