Yan ta'adda
Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da mutane uku bayan harbe wani dan banga a Barangoni da ke Bwari a babban birnin tarayya Abuja.
An yi garkuwa da Safiyanu Isa Andaha tare da wani Alhaji Adamu a yammacin ranar 1 ga Janairu, 2024 a hanyar Akwanga-Andaha. Jami'an tsaro sun bazama nemansu.
Wasu miyagun yan bindiga sun kai farmaki a jihar Nasarawa inda suka halaka mutum biyu. Jami'an yan sanda sun kuma cafke wani dalibin jami'a dauke da bindiga.
Hedikwatar rundunar tsaro (DHQ) ta sanar da cewa dakarun sojoji sun sheke yan ta'adda 6,886 da cafke 6,970 da ake zargi daga watan Janairu zuwa Disamban 2023.
Yan bindiga sun kai mummunan hari a kauyukan birnin tarayya Abuja da jihar Neja. A yayin harin yan bindigan sun halaka mutum hudu da sace wasu da dama
Wasu miyagun yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar Bwari ta birnin tarayya Abuja. Miyagun yan bindigan sun yi awon gaba da basarake da wasu mutum biyar.
Sheikh Ahmad Gumi ya ce kashe biliyoyin naira wajen siyo makaman da aka yi su a Yakin Duniya II don yaki da 'yan ta'adda tsohon yayi ne. Ya nemi a tattauna da su.
‘Yan bindiga za su hallaka daliban jami’ar Gusau da aka yi garkuwa da su. Nan da mako guda za a kashe daliban idan ba a fito da mutanensu da ke tsare ba.
Yan sanda sun tabbatar da cewa wasu gungun 'yan bindiga sun kai mummunan farmaki jihar Anambra. Sun kashe 'yan sanda biyu, sun sace masu zuwa bikin Kirsimeti.
Yan ta'adda
Samu kari