Dakarun Sojin Saman Najeriya Sun Halaka Yan Bindiga Sama da 100 a Zamfara

Dakarun Sojin Saman Najeriya Sun Halaka Yan Bindiga Sama da 100 a Zamfara

  • Jiragen yaƙin rundunar sojin saman Najeriya sun samu nasarar rage mugun iri inda suka halaka masu tarin yawa a jihar Zamfara
  • A harin da jiragen yaƙin sojin suka kai a kan ƴan bindigan waɗanda ke kan hanyar ke farmaki wasu ƙauyuƙa, sun sheƙe da dama daga cikinsu
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa sama da ƴan bindiga 100 ne aka ƙona a hsrin yayin da wasu da dama suka samu raunika

Jihar Zamfara - Sama da ƴan bindiga 100 ne suka mutu sakamakon harin da jiragen yaƙin rundunar sojin sama na 'Operation Hadarin Daji' (OPHD) suka kai a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Jaridar Channels tv ta tattaro cewa ƴan bindigan masu yawa suna kan hanyar su ne daga jihar Zamfara zuwa jihar Kebbi domin kai farmaki kan wasu ƙauyuka a ranar Talata, 10 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Wasu Garuruwa, Sun Halaka Babban Basarake a Jihar Arewa

Sojin sama sun halaka yan bindiga a Zamfara
Sojin sama sun halaka yan bindiga sama da 100 a Zamfara Hoto: Nigeria Airforce
Asali: Twitter

Ƴadda harin ya auku

Wata majiya mai ƙarfi daga ɓangaren sojoji ta bayyana cewa ƴan bindigan sun samu labarin akwai sojoji a kan hanyar, wanda hakan ya tilasta musu komawa yankin Dansadau a ƙaramar hukumar Maru ta jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar sojojin saman Najeriya, ta kai hare-hare kan ƴan ta'addan a ranar Talata, inda ta ƙona sama da 100 daga cikinsu tare da baburansu yayin da wasu da dama suka samu raunika daban-daban.

Rahotanni sun ce an gudanar da jana’izar ƴan ta'addan da aka kashe a dajin Sangeko da ke jihar Neja da kuma Babban Doka da ke ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Menene abin da hukumomi suka ce kan harin?

Da aka tuntubi kakakin 'Operation Hadarin Daji', Kyaftin Yahaya Ibrahim ya tabbatar da kai harin ta sama inda ya ƙara da cewa har yanzu ba a tantance adadin ƴan ta'addan da suka mutu ba.

Kara karanta wannan

Mutanen Gari Sun Halaka Hatsabibin Ɗan Bindiga, Sun Kwato Muhimmin Abu 150 a Jihar Arewa

Da yake mayar da martani, Daraktan hulɗa da jama'a da yaɗa labarai (DOPRI), na rundunar sojojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da kai hare-haren ta sama a jihar Zamfara.

Sai dai, bai bayyana ko adadin ƴan ta'adda nawa ba ne suka mutu.

"Eh, hakika, an kai hare-hare ta sama kan wasu ƴan ta'adda da ke tafiya, amma ba zan iya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ba." A cewarsa.

Yan Bindiga Sun Sace Malamin Addini

A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani malamin addinin musulunci a jihar Kogi a wani sabon hari.

Ƴan bindigan sun sace malamin ne tare da ɗan uwansa lokacin da suke raka gawa zuwa maƙabarta a ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel