Birtaniya a Shirye Take Ta Ba Isra’ila Gudunmawar Sojoji, Inji Firayinminista Sunak

Birtaniya a Shirye Take Ta Ba Isra’ila Gudunmawar Sojoji, Inji Firayinminista Sunak

  • Birtaniya ta yi alwashin taimakawa da Isra'ila da karfin soja wajen yakar dakarun Hamas na yankin Falasdinu
  • Wannan na zuwa ne bayan tashin hankalin da aka samu a karshen makon nan a yankin, inda mutane da dama suka mutu
  • Ba sabon abu bane samun sabani tsakanin Isra'ila da Falasdinu, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa

Biritaniya a shirye ta ke ta aike da tallafin soji ga kasar Isra'ila bayan harin da dakarun Hamas suka kai mata, in ji Firayiminista Rishi Sunak, Tribune Online ta ruwaito.

Ya ce ya yi magana da Benjamin Netanyahu kuma ya yi tayin aika masa "tallafin diplomasiyya ko ta tsaro" zuwa yankin idan ta kama.

Sunak ya ce Birtaniyya ta da kulla kawance da Isra'ila kuma Birtaniya na goyon bayanta wajen hakkinta na kare kai.

Kara karanta wannan

To fah: Isra'ila ta yi alwashin karar da dakarun Hamas, za ta ruguza gine-ginensu

Rishi Sunak zai tura soji Isra'ila
Birtaniya za ta tura sojoji Isra'ila | Hoto: Suzanne Plunkett
Asali: Getty Images

A cewarsa, daga goyon bayansa ga Isra'ila akwai samar da irin kayan aikin da ta ke bukara don amfani da su wajen kare kanta daga wadannan hare-hare na Hamas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya faro

Sama da mutane 100 ne aka yi garkuwa da su, yayin da 600 suka mutu bayan harin Hamas, in ji rahotanni daga Isra’ila, The Telegraph ta ruwaito.

Jiragen yakin IDF na Isra'ila da dama ne suka sauka a zirin Gaza a wani mataki na ci gaba da kai farmaki kan kungiyar Hamas.

Tun da farko, Sunak ya bayyana halin da ake ciki a Isra'ila a matsayin hadari, yana mai cewa babu wanda yake son ganin wani tashin hankali a yankin.

Ba sabon abu bane a samu sabani tsakanin Israa'ila da Falasdinu, lamarin da ya hallaka mutane babu adadi a yankin da ke da alaka da Larabawa.

Kara karanta wannan

Isra'ila Ta Dauki Fansa Kan Falasdinawa Bayan Hallaka Mutane 198, Ta Fadi Dalili

Zan karar da Hamas, inji firayinministan Isra'ila

A wani labarin, firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya lashi takobin kawo karshen dakarun Hamas tare da kawar da su bayan wasu hare-hare a ranar Asabar.

A cewar Netanyahu, Isra'ilawa za su ruguza Hamas tare da daukar fansa da karfi iko a yakin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin kasashen biyu.

Firayim Ministan ya ce dakarun Hamas suna da burin kashe dukkan 'yan Isra'ila amma gwamnatinsa ba za ta bari su yi nasara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel