Yan ta'adda
Wasu miyagun yan bindiga sun kai sabon hari jihar Katsina suka halaka jami'an yan sanda da ke a bakin aiki. Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da makamai.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya gargadi shugabannin kananan hukumomin Abuja kan gaza halartar taron tsaro na wata wata da ake yi a majalisar kananan hukumomin Abuja.
Sanata Shehu Sani ya zayyana yadda jihohin Arewa ke fama da hare-haren 'yan ta'adda, fadan kabilanci da ma na addini wanda ya gusar da zaman lafiya a shiyyar
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kabilar Jukun ne sun kai hari tare da kashe wasu ‘yan gudun hijira biyu da suka dawo gida a Ikyenum a ranar Alhamis.
Wani DPO na ‘yan sanda ya ki amincewa da karbar cin hancin naira miliyan daya da wani dan bindiga ya ba shi bayan an kama shi a wani otal da ke garin Kaduna.
Al'ummar da ke zaune a karamar hukumar Mangu da ke jihar Filato sun zargi jami'an tsaron jihar na 'Operation Rainbow' da aikata laifukan kisan kai da kona gidaje.
Wasu miyagun yan bindiga dauke da makamai sun kai wani sabon hari a jihar Benue. Yan bindigan a yayin farmakin na su sun salwantar da rayuka tare da tafka barna.
Kungiyoyin 'yan ta'adda na ISWAP da na Boko Haram sun yi wani kazamin fada a tsakaninsu, wanda ya yi silar mutuwar mutane da dama a Tafkin Chadi.
Dakarun sojoji sun samu nasarar ragargazar yan ta'adda a jihar Kebbi. Dakarun sojojin sun kuma ceto mutanen da yan ta'addan suka yi garkuwa da su.
Yan ta'adda
Samu kari