DHQ: Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'adda 715 da Ceto Mutum 465 a Najeriya

DHQ: Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'adda 715 da Ceto Mutum 465 a Najeriya

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara kan ƴan ta'adda masu tada ƙayar baya a cikin watan Afirilun shekarar 2024
  • Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa sojojin sun hallaka ƴan ta'adda 715 tare da ceto mutum 465 da aka yi garkuwa da su a cikin watan
  • Sojojin sun kuma kai hare-hare a sansanonin shugabannin ƴan ta'adda masu yawa ciki har da na Bello Turji da ke dajin Kagara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ce dakarun sojoji sun hallaka jimillar ƴan ta'adda 715 tare da ceto mutum 465 da aka yi garkuwa da su a hare-haren ƙasa da na sama a faɗin ƙasar nan a cikin watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi nasara kan 'yan ta'adda a jihohin Katsina da Plateau

Daraktan harkokin yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Abuja.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda
Dakarun sojoji sun salwantar da ran 'yan ta'adda 715 Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Ya ƙara da cewa sojojin sun kuma kama mutane aƙalla 1,146 da ake zarginsu da aikata laifuka a cikin watan, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun farmaki ƴan ta'adda

Manjo Janar Edward Buba ya ce an kai hare-haren bam a sansanonin wasu shugabannin ƴan ta’adda da suka haɗa da Nasanda, Babaru, Kamilu Buzaru, Ali Dawud, Bakura Fallujah da Mallam Ari, rahoton Vanguard ya tabbatar.

A cewarsa, sauran shugabannin ƴan ta’addan da aka kai musu farmaki ta sama sun haɗa da Mallam Yadee a ƙaramar hukumar Mariga ta Neja da sansanin Bello Turji da ke dajin Kagara a tsakanin Shinkafi a Zamfara da ƙaramar hukumar Isa a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Rundunar sojojin sama ta ragargaji 'yan ta'adda a jihar Neja

"Hare-haren haɗin gwiwar tsakanin dakarun ƙasa da na sama ya sanya an hallaka sama da ƴan ta'adda 715, an cafke waɗanda ake zargi mutum 1,146 tare da ceto mutum 465 da aka yi garkuwa da su."
"Hakazalika, dakarun sojojin sun ƙwato makamai 937, harsasai 23,034 da hana satar man fetur wanda aka yi ƙiyasin kuɗinsa sama da N2bn."

- Manjo Janar Edward Buba

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na rundunar sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro na farin kaya (DSS) sun hallaka ƴan ta'adda bakwai a jihar Sokoto.

Jami'an tsaron sun samu wannan gagarumar nasarar ta hallaka ƴan ta'addan ne a yankin Modachi da ke ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel