An Tsere da Sarki: Yan Bindiga Sun Kai Hari Fada a Zamfara, Sun Hallaka Mutane 3

An Tsere da Sarki: Yan Bindiga Sun Kai Hari Fada a Zamfara, Sun Hallaka Mutane 3

  • An shiga fargaba yayin da wasu 'yan bindiga suka farmaki garin Zurmi hedkwatar karamar hukumar Zurmi a Zamfara
  • Maharan sun kai harin ne a daren jiya Laraba 24 ga watan Afrilu inda suka kutsa kai fadar Sarkin Zurmi da ke jihar
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani mazaunin garin Zurmi inda ya tabbatar da faruwar harin da miyagun suka kai a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - 'Yan bindiga sun farmaki hedkwatar karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara a daren jiya Laraba 24 ga watan Afrilu.

Maharan sun kutsa kai har cikin fadar Sarkin Zurmi a kokarin sace basaraken, Alhaji Muhammad Bunu inda ba su yi nasara ba.

Kara karanta wannan

Neja: 'Yan ƙauye sun shiga ɗimuwa bayan sojoji sun fece tare da barinsu a hannun 'yan bindiga

Yan bindiga sun farmaki fadar Sarki a Zamfara yayin da suka bindige wasu
Yan bindiga sun sake kai hari a jihar Zamfara inda suka tafka barna. Hoto: Dauda Lawal Dare.
Asali: Twitter

Yadda 'yan bindiga suka kai harin Zamfara

Wani mazaunin yankin, Malam Aminu Sale ya bayyanawa Vanguard cewa maharan sun kai hari fadar Sarkin ne inda suka yi ta harbi sama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ya ce jami'an tsaro sun yi nasarar tserewa da basaraken zuwa birnin Gusau da ke jihar, cewar Leadership.

Majiyar ta ce bayan maharan sun yi rashin nasara wurin sace basaraken, sun lalata karfunan sabis na MTN da tiransfoma a yankin.

Maharan sun hallaka mutum 3 a Zamfara

Hakan ya kawo daukewar sabis na kamfanin wanda ya sake jefa mutanen yankin a cikin masifa bayan harin da suka kai.

Har ila yau, maharan sun hallaka wasu mutane uku da suka yi garkuwa da su yayin harin da suka kai.

Maharan wadanda suka kai harin da misalin karfe 11:00 sun kuma kai hari gidan tsohon gwamnan Nasarawa a mulkin soja, Kanal Bala Mande mai ritaya.

Kara karanta wannan

Fursunoni 118 sun tsere daga gidan gyaran hali a jihar Neja, an samu bayanai

Martanin mazaunin yankin ga Legit Hausa

Legit Hausa ta ji ta bakin wani mazaunin garin Zurmi inda ya tabbatar da faruwar harin da miyagun suka kai a yankin.

Ibrahim Rabiu ya yi Allah wadai da harin 'yan bindiga a Zurmi inda ya tabbatar da cewa maharan sun lalata karfunan sabis na kamfanin MTN.

"Abin da ya faru jiya abu ne marar dadi yadda ɓarayi suka mamaye garin Zurmi, harbe-harbe kawai ka ke ji ta ko ina."
"Amma cikin iyawar Allah sun kashe mutum uku kuma sun tafi da mutum biyu inda suka farmaki masaraurar Zurmi tare da garkuwa da wani mai rike da saraurar Shamaki."

- Ibrahim Rabiu

An dakatar da kwamandan tsaro a Zamfara

A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da kwamandan hukumar CPG a jihar, Kanal Rabi'u Garba mai ritaya.

Gwamnatin ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnati, Abubakar Nakwada ya fitar a makon da ya gabata.

Nakwada ya bayyana haka a jiya Laraba 17 ga watan Afrilu inda ya ce dakatarwar kwamandan hukumar CPG ta fara aiki nan take.

Asali: Legit.ng

Online view pixel