Hare Haren 'Yan Bindiga: Basarake a Zamfara Ya 'Tona' Asirin Masu Ruruta Ta'addanci

Hare Haren 'Yan Bindiga: Basarake a Zamfara Ya 'Tona' Asirin Masu Ruruta Ta'addanci

  • Mai Martaba Sarkin Kwatarkwashi a jihar Zamfara ya tona asirin wadanda ke ingiza wutar ta'addanci musamman a Arewacin Najeriya
  • Abubakar Ahmed Umar ya zargi 'yan kasashen ketare da ruruta matsalar inda suke kashe mutane tare da kwashe dukiyar al'umma
  • Sarkin ya kuma ce babban dalilin matsalar tsaron musamman a jihar Zamfara shi ne ma'adinai da ke tattare a yankin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Yayin da ake fama da hare-haren 'yan bindiga a Zamfara, babban basarake ya fadi dalilan da ke ruruta matsalar a tunaninsa.

Sarkin Kwatarkwashi, Mai Martaba, Abubakar Ahmed Umar ya zargi 'yan kasashen ketare da tattalin arzikin ma'adinai a yankin da haddasa matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Katsina: An shiga makoki bayan 'yan bindiga sun hallaka shugaban APC da wani mutum

Basarake ya bayyana wadanda suka jawo matsalar tsaro a Arewa
Yayin da rashin tsaro ya yi ƙamari, Sarkin Kwatarkwashi ya tona asirin masu ruruta matsalar a Arewa. Hoto: @HQNigerianArmy.
Asali: Twitter

Musabbabin matsalar tsaro a Arewa

Sarkin ya ce wadannan abubuwa biyu su ne musabbabin matsalar tsaron jihar Zamfara da ma yankin Arewacin Najeriya gaba daya, cewar Zagazola Makama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce tun farko matsalar Fulani da Hausawa ne sila amma daga bisani samun gwal da sauran ma'adinai sun kara jefa yankin a cikin wani hali, cewar rahoton PRNigeria.

"Maganar gaskiya shi ne akwai saka hannun 'yan kasashen ketare a matsalar tsaron Arewacin Najeriya."
"Duk lokacin da aka kashe Fulani masu ɗauke da makamai ƙaruwa suke yi, yau sojoji za su hallaka su, gobe za su karu su kuma su farmaki mutane tare da hallaka su."
"Suna zuwa daga Mali da Burkina Faso su hallaka mutanenmu kuma su kwashe mana dukiya."

- Abubakar Ahmed Umar

Wace shawara ya bayar kan matsalar tsaro?

Kara karanta wannan

Kamfanin NNPC ya shawo kan matsalar da ta kawo dogon layi a gidajen mai

Sarkin ya bukaci hadin kan gwamnatoci a dukkan matakai domin kawo karshen wannan matsala a Arewacin Najeriya.

Ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta karo jami'an tsaro a yankin da kuma tabbatar da walwalarsu domin samun abin da ake nema.

Yan bindiga sun kai hari a Zamfara

A wani labari, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kai mummunan hari a garin Zurmi hedkwatar karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Maharan sun kutsa kai cikin fadar Sarkin garin inda jami'an tsaro suka yi nasarar tsarewa da basaraken zuwa birnin Gusau da ke jihar.

Yayin kai harin, maharan sun hallaka mutane uku tare da lalata karfunan sabis na kamfanin MTN a yankin da ya jawo matsala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel