'Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'an CJTF 9 a Wani Mummunan Hari a Sokoto

'Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'an CJTF 9 a Wani Mummunan Hari a Sokoto

  • Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai sabon harin ta'addanci a jihar Sokoto kan jami'an ƴan sa-kai na CJTF a ƙaramar hukumar Isa
  • Miyagun sun hallaka jami'an tsaron na CJTF guda tara sannan suka raunata wasu da dama bayan sun yi musu kwanton ɓauna
  • Wani majiya daga ɓangaren ƴan sa-kan ya tabbatar da cewa an kuma yi garkuwa da wasu jami'ai guda uku a yayin mummunan harin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Ƴan bindiga sun hallaka aƙalla jami’an ƴan sa-kai na CJTF guda tara a wani mummunan hari a jihar Sokoto.

Ƴan bindiga sun hallaka ƴan sa-kan ne a wani harin kwanton ɓauna da suka kai musu wanda ya kuma yi sanadiyyar raunata jami'an da ba a tantance adadinsu ba.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi nasara kan 'yan ta'adda a jihohin Katsina da Plateau

'Yan bindiga sun hallaka jami'an CJTF
'Yan bindiga sun yi wa jami'an 'yan sa-kai na CJTF kwanton bauna a Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da wasu jami’an ƴan sa-kan na CJTF guda uku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Wani majiya ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata a ƙaramar hukumar Isa ta jihar.

Majiyar na CJTF ya ƙara da cewa ƙaramar hukumar Isa ta kasance tungar ƴan ta’adda kuma tana da matukar hatsari ga jami’an tsaro.

A kalamansa:

"Mun rasa mambobi tara a wani harin kwanton ɓauna da aka kai a ƙaramar hukumar Isa, wasu da dama sun samu raunuka."
"An kuma yi awon gaba da wasu guda uku a harin bayan da jami'anmu suka samu kiran gaggawa na tallafawa jami’an tsaro. Mun samu labarin baƙin cikin kwanaki biyu da suka wuce."

Wannan shi ne karo na biyu da ƴan bindiga su ke yi wa jami’an CJTF kwanton ɓauna a jihar Sokoto cikin watanni biyu.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun yi nasarar dakile harin 'yan bindiga a jihar Katsina

Bam ya hallaka jami'an CJTF

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani bam da ƴan ta'addan ISWAP suka dasa ya salwantar da rayukan jami'an ƴan sa-kai na CJTF guda biyar a jihar Borno.

Lamarin wanda ya auku a ƙaramar hukumar Dikwa ta jihar ya kuma jawo wasu jami'ai gudu uku sujn samu raunuka bayan motarsu ta taka bam ɗin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel