Rikicin APC a Kano: Tsagin Shekarau ya yi fatali da yunkurin sulhun uwar jam'iyya

Rikicin APC a Kano: Tsagin Shekarau ya yi fatali da yunkurin sulhun uwar jam'iyya

  • Tsagin Sanata Ibrahim Shekarau a jihar Kano ya yi fatali da yunkurin sulhun da uwar jam'iyyar APC ke kokarin musu da tsagin Ganduje a Kano
  • Shekarau ya zargi uwar jam'iyyar da rashin adalci ta yadda ta shugabantar da Ganduje a yayin sulhun, ya ce hakan bai dace ba
  • A cewar Shekarau, sun fara ganin takardar sanarwar sulhun da za a yi ne a kafafen sada zumunta tun kafin ta iske su

Kano - Rikici na cigaba da rincabewa na shugabancin jam'iyyar APC a jihar Kano. Bangaren Sanata Shekarau sun yi fatali da sanarwar da uwar jamiyya ta bayar na yunkurin sasanta su.

Babu shakka wannan boren da tsagin Shekarau ke yi ya na da alaka da yadda aka jagorantar da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar a kwamitin sulhun.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Sarkin Jama'are, Dakta Ahmadu Muhammad Wabi ya riga mu gidan gaskiya

Rikicin APC a Kano: Tsagin Shekarau ya yi fatali da yunkurin sulhun uwar jam'iyya
Rikicin APC a Kano: Tsagin Shekarau ya yi fatali da yunkurin sulhun uwar jam'iyya. Hoto daga bbc.com
Asali: UGC

A wata tattaunawa da BBC ta yi bayan fitar sanarwar uwar jam'iyyar, Sanata Shekarau ya ce sun yi fatali da sanarwar kuma ba su aminta da ita ba.

"Mu na da mataki guda 3 a wannan sanarwar: A duk zama da aka yi sau 2 ko 3, wanda Gwamna Ganduje ya halarta da mukarrabansa kuma muka je, karkashin shugabancin Gwamna Mai Mala Buni, shugaban jam'iyyar na kasa.
"An nemi kowanne tsagi ya bayyana abinda suke son a yi da shawarar warware matsalar, kowa ya bayar da na shi. Shugaban jam'iyya ya ce za su koma su duba bayanan da muka yi domin fito da matsaya tare da shawartar abinda ya dace a yi," Shekarau yace.

Shekarau ya kara da cewa, a sanarwar jam'iyyar, ba ta yi magana kan matsayar da bangarorin 2 suka cimma ba, kuma jam'iyya ba ta fadi komai da bangarorin suka bukata ba.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

Shekarau ya ce abu na 2 kafin fitar takardar, an kai wa Ganduje takardar kafin a kai masa wanda hakan bai dace ba.

Ya kara da cewa, takardar ta shiga duniya inda aka ganta a kafafen sada zumunta kafin a kawo masa.

"Ta yaya mutane biyu suna jayayya zama sai a shugabantar da daya daga cikinsu a sasancin, alhalin a waccan sasancin shi ya jagoranta, a gaskiya muna ganin an zalince mu kuma ba za a yi adalci ba," Shekarau ya kara da cewa.

Kano: APC ta kafa kwamitin sulhu, ta nada Ganduje matsayin shugaban jam'iyya

Uwar jam'iyyar APC ta kasa ta kafa kwamitin mutum 5 na hadin guiwa wanda zai tabbatar da an shirya sabon tsari na magance rikicin jam'iyyar na cikin gida a jihar Kano.

Kwamitin zai samu shugabancin Gwamna Abdullahi Umar ganduje na jihar Kano tare da Sanata Ibrahim Shekarau a matsayin mataimakinsa.

Ganduje da Shekarau ba su ga maciji kan yadda ake tafiyar da al'amuran jam'iyyar a jihar, inda suka rabe tare da fitar da shugabannin jam'iyyar a kowanne tsagi, lamarin da ya sake jefa su cikin rikici.

Kara karanta wannan

Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

Asali: Legit.ng

Online view pixel