Takardun Kotu Sun Fito, An Ga Dalilin Cire Aminu Gwarzo daga Jerin Yan Takarar Gwamnan Kano

Takardun Kotu Sun Fito, An Ga Dalilin Cire Aminu Gwarzo daga Jerin Yan Takarar Gwamnan Kano

  • Takardun kotu sun tabbatar da cewa INEC ta hana wallafa sunan Aminu Gwarzo bisa umarnin wucin gadi na Babbar Kotun Tarayya
  • Mambobin NDC uku ne suka shigar da ƙara kan yadda aka zaɓi Gwarzo da abokin takararsa, Mustapha Rabiu Kwankwaso
  • Kotu ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 16 ga Nuwamba, 2026, bayan Gwarzo ya nemi a shigar da shi cikin shari’ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Takardun da suka fito, waɗanda aka tabbatar da sahihancinsu daga Babbar Kotun Tarayya sun yi bayani kan cire sunan Aminu Abdussalam Gwarzo daga yan takarar gwamnan Kano.

Takardun sun tabbatar da cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta hana wallafa sunan ɗan takarar gwamnan jam’iyyar NDC bisa bin umarnin wucin gadi da kotu ta bayar.

Kara karanta wannan

Aminu Abdulsalam ya bayyana mutanen da yake zargi da yunkurin hana shi takara a Kano

Aminu Gwarzo.
Kotu ta hana INEC wallafa sunan ɗan takarar gwamnan NDC a Kano
Source: Facebook

Dalilin INEC na cire sunan Gwarzo

Tribune Nigeria ta rahoto cewa takardun, waɗanda suka shafi ƙara mai lamba FHC/KN/CS/440/2026, sun nuna cewa kotu ta hana INEC wallafa sunan kowane ɗan takara a jerin ’yan takarar gwamna na NDC a zaɓen Kano na 2027.

Kotun ta dakatar da sanya sunan Aminu Gwarzo ne har sai an saurari wata muhimmiyar buƙata da aka gabatar a gabanta.

Mambobin NDC uku da ba su gamsu da yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani ba ne suka shigar da ƙarar.

Mambobin NDC sun kai kara kotu

Wadanda suka shigar da karar au ne Garba Umar Isa, Yau Nasiru da Atiku Jamilu Abubakar, inda suka bayyana INEC da jam’iyyar NDC a matsayin wadanda suke kara.

Masu ƙarar sun garzaya kotu ne kan wata buƙata da amsua gabatar ba tare da sanar da ɓangaren da ake ƙara ba.

Sun ƙalubalanci tsarin da aka bi wajen zaɓen ɗan takarar gwamnan jam’iyyar NDC a jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, da abokin takararsa, Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

An kama mutum 3 kan zargin ƙona motar yan tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC

Rahotanni sun nuna cewa masu ƙarar sun soki abin da suka bayyana a matsayin matakin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya, ya ɗauka shi kaɗai na zaɓar Gwarzo da ɗansa Mustapha.

A hukuncin da ya yanke a ranar 27 ga Oktoba, 2026, Mai Shari’a Amobeda ya umarci INEC, jami’anta da wakilanta da su guji wallafa sunan kowane ɗan takara a matsayin dan takarar gwamna na NDC a Kano har sai an yanke hukunci kan buƙatar da aka sanar da ɓangarorin.

Mai Shari’a Amobeda ya kuma bayar da umarnin miƙa wa waɗanda ake ƙara takardar umarnin kotun da sauran takardun shari’ar, tare da cewa a gaggauta sauraron ƙarar.

Aminu Gwarzo.
Dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin inuwar jam'iyyar NDC, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo Hoto: Aminu Abdussalam Gwarzo
Source: Facebook

Kotu ta ɗage sauraron ƙarar

Da farko, kotu ta ɗage shari’ar zuwa ranar 2 ga Nuwamba, 2026, domin sauraron ƙarar. Sai dai ba a samu damar ci gaba da shari’ar a ranar Litinin ba, bayan lauya Gwarzo ya gabatar da buƙatar neman a shigar da shi cikin waɗanda ke cikin shari’ar.

Bayan wannan ci gaba, kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 16 ga Nuwamba, 2026.

Aminu Gwarzo ya zargi gwamnatin Kano

Kun ji cewa dan takarar gwamna na NDC, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya zargi gwamnatin jihar Kano da ƙoƙarin hana shi shiga zaɓen gwamna na shekarar 2027.

Gwarzo ya yi zargin cewa wasu jami’an gwamnatin jihar sun haɗa kai da wasu mutane masu alaƙa da jam’iyyar APC wajen shirya shigar da ƙara a kotu domin hana INEC wallafa sunansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262