Wata Sabuwa: An Fara Yunkurin Kwace Kujerun Yan Majalisa 45 da Suka Sauya Sheka
- Jam’iyyar NNPP ta shigar da kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan sauya shekar ’yan majalisa 45 da aka zaba karkashinta a 2023
- Jam’iyyar ta bukaci kotu ta fassara tanade-tanaden kundin tsarin mulki da suka shafi sauya sheka da kuma yiwuwar rasa kujerun majalisa
- NNPP ta ce ba ta hade da wata jam’iyya ba, kuma ba ta daina kasancewa jam’iyyar siyasa mai rajista ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jam’iyyar NNPP ta maka Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da wasu ’yan majalisa 45 a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
NNPP ta shigar da wannan kara ne kan sauya shekar ’yan majalisar da aka zaba karkashin inuwar jam’iyyar a zaben 2023.

Source: Facebook
Premium Times ta rahoto cewa NNPP ta shigar da karar ne ta hannun lauyoyinta na kamfanin Lex Firma LP.

Kara karanta wannan
PRP ta yi kaca kaca da shirin Tinubu, ta taɓo batun kisan Sheikh Yahaya Masussuka
NNPP ta maka yan Majalisa 45 a kotu
Ta nemi kotu ta fassara tare da tabbatar da aiwatar da tanade-tanaden kundin tsarin mulki da suka shafi sauya shekar zababbun ’yan majalisa daga jam’iyyun da suka tsaya takara a karkashinsu.
A cikin bayani da aka shigar domin goyon bayan karar, NNPP ta kalubalanci sauya shekar ’yan majalisa 45, wadanda suka hada da mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Majalisar Wakilai ta Tarayya da kuma Sanatoci da aka zaba karkashinta.
Jam’iyyar ta kara da cewa tuni INEC ta saka sunayen wasu daga cikin ’yan majalisar a matsayin ’yan takarar wasu jam’iyyu a zaben 2027.
Wannan lamari, a cewarta, ya haifar da tambayoyi kan sahihancin takarar tasu da kuma ci gaba da rike kujerun da suke kai a yanzu..
Tanade-tanaden kundin tsarin mulki
Jam’iyyar ta ce tana neman kotu ta yanke hukunci kan abin da kundin tsarin mulki ya tanada game da sauya sheka, musamman sashe na 68(1)(g), 68(2), 109(1)(g) da 109(2).
A cewar NNPP, wadannan sassa sun bayyana yanayin da yan majalisar tarayya da majalisun dokokin jihohi za su iya rasa kujerunsu bayan sauya sheka, bisa la’akari da kebantattun sharuddan da kundin tsarin mulki ya amince da su.

Source: Getty Images
''Muna kuma son a sanar da majalisunnda abin ya shafa game da sauya shekar, sannan a dauki matakan da kundin tsarin mulki ya tanada, ciki har da yiwuwar ayyana kujerun a matsayin babu kowa da gudanar da zaben cike gurbi," in ji NNPP.
A cewar jam’iyyar, ’yan siyasar sun koma wasu jam’iyyu kuma suna neman cimma burinsu na siyasa gabanin babban zaben 2027, ba tare da kammala matakan murabus din da ake bukata ba.
Majalisa ta gayyaci shugaban INEC
Kun ji cewa Majalisar Wakilai ta gayyaci shugaban INEC domin ya yi bayani kan shirye-shiryen gudanar da babban zaɓen 2027.
An ɗauki matakin ne bayan wani ƙuduri da ’yan majalisa guda biyu, Hon. Mansur Soro, mai wakiltar jam’iyyar APM daga Bauchi, da Hon. Abdussamad Dasuki, na ADC daga Sokoto, suka gabatar tare.
Asali: Legit.ng
