Atiku Ya Yabi Bala Mohammed kan Tarbar da Ya Masu a Bauchi da Ya Je Kamfen
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar da tawagar shi sun isa jihar Bauchi domin gudanar da yakin neman zabe
- Atiku Abubakar da abokin takarar shi a ADC, Rotimi Amaechi sun ziyarci fadar mai martaba Sarkin Bauchi ranar Juma'a da yamma
- A bayanan da ya yi a fadar sarkin, Atiku ya yi godiya ga gwamna Bala Mohammed kan yadda ya bari suka shiga garin lami lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya yaba wa gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed.
Atiku ya yaba wa Bala Mohammed ne kan yadda ya ba shi hadin kai wajen gudanar da kamfen din ADC a jihar Bauchi ba tare da wata matsala ba.

Source: Twitter
Legit ta tattaro bayanan da Atiku ya yi ne a wani bidiyo da Umar Bello Tafida ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma'a.
Atiku ya godewa Bala Mohammed
Atiku ya bayyana cewa ya yi amfani da damar ganawa da sarkin ya godewa Bala Mohammed bisa karrama shi da tawagar shi da ya yi.
Ya ce:
"Domin wurare da yawa idan mun je ba a barin mu mu gana da sarakunan mu. Ba a barin mu mu ba su darajarsu."
Dan takarar ya kara da cewa shugabannin siyasa da suka saba jam'iyya da su suna kulle sarakunan su hana su ganawa da su.
Atiku ya fadi abin da ya faru da wani limami da ya yi sallah a masallacin shi a wata jiha da cewa:
"Limamin masallacin da na yi sallah sai aka ce gwamna ya dakatar da shi"
Wazirin Adamawa ya ce abin da suka sani shi ne limamai suna karkashin sarakuna ne a bisa al'ada ba karkashin gwamna ba, amma yanzu abin ya lalace.

Source: Facebook
Ya kara da cewa rashin ladabi ne ya jefa 'yan siyasa cikin irin wannan yanayi da cin mutuncin sarakuna, kuma ba zai yi haka ba idan ya samu nasara a 2027.
Atiku ya yabi sarkin Bauchi
Yayin da yake magana game da Sarkin Bauchi, mai martaba Alhaji Rilwanu Sulaimanu Adamu, Atiku ya bayyana cewa ya dauki fadar Bauchi kamar gidan shi ne.
Dan takarar ya bayyana cewa a kowane lokaci ya samu damar shiga jihar Bauchi yana ya da zango a fadar sarkin domin kai ziyara ta ban girma.
Ya kuma tabbatar da cewa zai cigaba da girmama sarakunan gargajiya a Bauchi da sauran jihohin Najeriya kamar yadda ya ke a tarihi.
Tinubu ya gargadi 'yan siyasa
A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga 'yan siyasa su daina tayar da tarzoma yayin yakin neman zabe.
Shugaban kasar ya bayyana cewa ya kamata a mayar da hankali kan neman kuri'a ta hanyar bayyana abubuwan da za a yi maimakon tashin hankali.
Kalaman Bola Tinubu na zuwa ne bayan wani farmaki da aka kai wa dan takarar PDP a Gombe, Sheikh Isa Pantami da wasu 'yan NDC a Legas.
Asali: Legit.ng

