2027: Jigon NDC Ya Dawo da Maganar Hadakar Atiku da Peter Obi

2027: Jigon NDC Ya Dawo da Maganar Hadakar Atiku da Peter Obi

  • Daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na NDC, Ibrahim Abdulkarim, ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya haɗa kai da Peter Obi
  • Abdulkarim ya ce Kwankwaso ya ajiye burinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa domin aiki tare da Obi, yana mai cewa sauran shugabannin hamayya suna da damar shiga haɗakar
  • Ya kuma yi alƙawarin cewa NDC za ta kare ƙuri’un masu zaɓe a 2027, tare da cewa Obi zai zaɓi ƙwararrun mutane bisa cancanta idan ya zama shugaban ƙasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Ibrahim Abdulkarim, ya buƙaci shugabannin hamayya, ciki har da Atiku Abubakar, su haɗa kai da Peter Obi gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan

Masu shirin magudin zabe sun shiga uku, Obi ya yi masu barazana ga INEC

Abdulkarim ya bayyana hakan ne yayin wata, inda ya ce haɗakar hamayyar ta riga ta fara, tare da Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa da Kwankwaso ya amince ya yi aiki tare da shi.

Peter Obi da Atiku Abubakar
Peter Obi a hagu da Atiku Abubakar a dama. Hoto: Peter Obi|Rabiu Musa Kwankwaso
Source: UGC

Arise News ta wallafa cewa ya ce sauran shugabannin siyasa suna da damar shiga haɗakar domin ƙara wa ’yan adawa ƙarfin samun nasara a zaɓen.

Ana so Atiku Abubakar ya shiga haɗakar OK

Abdulkarim ya bayyana cewa ba lallai ne haɗakar ’yan adawa ta kasance a ƙarƙashin jam’iyyar ADC ba, yana mai cewa za a iya gina ta a ƙarƙashin NDC.

Ya ce Kwankwaso ya ajiye burinsa na takarar shugaban ƙasa domin mara wa Obi baya, kuma suna son sauran ’yan siyasa su bi wannan hanya.

A kalamansa:

“Dole ne ’yan adawa su haɗa kai domin mu yi nasara. Tuni ’yan adawa suka fara haɗuwa. Babu wanda ya ce dole sai haɗakar ta kasance a ƙarƙashin ADC.
"Za ta iya kasancewa a NDC, kuma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya riga ya ajiye burinsa na takara.
“Abin da muke nema shi ne sauran mutane su shiga tare da mu, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, domin mu samu faɗin goyon bayan da suke ganin za su iya ƙarawa.”

Kara karanta wannan

Obi ya bukaci Bola Tinubu ya koma gida ya huta, ya bar maganar takarar 2027

Ya ƙara da cewa idan sauran shugabannin hamayya ba su shiga haɗakar ba, NDC za ta ci gaba da tafiyar da shirinta na siyasa.

Peter Obi da Kwankwaso
Dan takarar NDC, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Twitter

Tsarin siyasar jam'iyyar NDC

Da yake magana kan sukar tsarin yaƙin neman zaɓen NDC da shirin jam’iyyar na zaɓen 2027, Abdulkarim ya ce bai kamata a rikita jam’iyyar da ƙungiyoyin magoya bayan Obi da aka fi sani da Obidient ba.

Ya bayyana cewa jam’iyyar tana da tsarin ta, yayin da ƙungiyoyin magoya baya da dama ke aiki tare da ita.

Abdulkarim ya ce:

“Ta yaya za ku kwatanta jam’iyyar siyasa da ƙungiyar goyon baya? Ba mu da wata matsala da hakan. Dukkansu suna cikin jam’iyyar NDC. Muna da ƙungiyoyin goyon baya sama da dubu.”

Ya bayyana cewa waɗannan ƙungiyoyi za su taimaka wajen faɗaɗa goyon bayan jam’iyyar da wayar da kan masu zaɓe a faɗin ƙasar.

Peter Obi ya soki Bola Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya bar mulki a shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Atiku ya ce zai janye wa Obi takara idan aka cire Kwankwaso daga mataimaki?

Tsohon gwamnan Anambra ya bayyana cewa Najeriya na buƙatar shugaban ƙasa mai ƙoshin lafiya da kuzarin fuskantar matsalolin tattalin arziki da tsaro.

Obi ya bayyana hakan ne a Abuja yayin ƙaddamar da majalisar kamfen ta ƙasa ta NDC, inda ya zargi gwamnatin APC da ƙara ta’azzara talauci, rashin aikin yi, cin hanci da rashawa da matsalar tsaro.

Wanda ya tantance Ibrahim Yusuf, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng