Atiku Ya Kunno Wuta, Kotu Ta Shirya Yanke Hukunci da Ake Son Hana Tinubu Takara
- Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar yanke hukunci kan bukatar Atiku Abubakar ta gyara karar da ya shigar kan Tinubu da APC
- Atiku da ADC na neman kotu ta soke cancantar Tinubu da APC shiga zaben shugaban kasa na 2027
- Tinubu, APC da INEC sun bukaci kotu ta yi watsi da bukatar gyaran karar, suna masu cewa lokacin shigar da karar ya wuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Mai shari’a Inyang Ekwo na Kotun Tarayya da ke Abuja ya sanya rana domin yanke hukunci kan bukatar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya shigar.
Atiku ya bukaci gyara karar da ya shigar kan Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC domin hana shi rakara a zaben 2027.

Source: Facebook
Mai shari’ar ya sanya ranar 20 ga watan Nuwambar 2026 bayan lauyan Atiku, Joseph Silas, da lauyoyin wadanda ake kara sun gabatar da hujjojinsu kan bukatar gyaran karar, cewar Vanguard.
Korafin Atiku, ADC da ke gaban kotu
A cikin babbar karar, Atiku da ADC sun bukaci mai shari’a Ekwo ya hana Shugaba Tinubu da APC shiga zaben shugaban kasa na 2027.
Sun kalubalanci takardar shaidar kammala bautar kasa ta NYSC da Tinubu ya gabatar wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta hannun APC.
Masu karar, wadanda suka shigar da kara kan shugaban kasa, APC da INEC, sun zargi APC da gabatar wa INEC takardar shaidar NYSC ta shugaban kasa da suka ce an kirkira ta hanyar jabu.
Saboda haka, sun bukaci kotu ta umarci INEC ta cire sunayen Tinubu da APC daga jerin sunayen ‘yan takara da jam’iyyun da za su shiga zaben shugaban kasa na 2027.
Sai dai bayan wadanda ake kara sun shigar da takardun kare kansu, Atiku da ADC sun sake komawa kotu domin neman izinin gyara karar, bisa wasu kura-kurai da suka ce sun gano.

Source: Facebook
Yadda zaman kotun ya gudana
A lokacin da aka kira karar a ranar Talata, lauyan Atiku Abubakar, Silas, ya shaida wa kotun cewa an sanya shari’ar ne domin sauraron bukatarsu ta gyara takardar karar farko.
Lauyan Tinubu, Wole Olanipekun (SAN), lauyan APC, Akin Olujinmi (SAN), da lauyan INEC, Alex Izinyon (SAN), sun shaida wa kotun cewa suna shirye domin ci gaba da sauraron bukatar.
Yayin da yake gabatar da bukatar gyaran karar, Silas ya ce an rubuta takardar bukatar ne a ranar 4 ga Satumba, sannan aka shigar da ita a ranar 10 ga Satumba.
Ya ce bayan sun karbi takardun kare kansu da wadanda ake kara suka gabatar kan bukatarsu, sun mayar da martani ta hanyar rubutacciyar hujjar shari’a.
Tinubu ya bukaci kotu ta yi watsi da bukatar
Da yake mayar da martani, Olanipekun ya ce sun shigar da takardar rantsuwar amsa mai sakin layi tara a madadin shugaban kasa.
Ya bukaci kotun ta yi watsi da bukatar Atiku, yana mai cewa kotun ba ta da hurumin amincewa da ita.
Babban lauyan ya kuma ce dokar da ta kayyade lokacin shigar da kara ta hana Atiku gabatar da bukatar a wannan mataki.
A cewarsa, abin da masu karar ke kokarin yi ba gyara karar da suka shigar ba ne, sai dai shigar da sabuwar kara.
Bola: APC ta caccaki Atiku
An ji cewa Jam’iyyar APC ta zargi tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da barin burin siyasa ya rinjayi yadda yake mu’amala da Shugaba Bola Tinubu.
Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben APC, Dele Alake, ya ce kiran shugaban kasar da “Bola” maimakon amfani da mukaminsa bai dace ba.
APC ta ce za ta mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi ’yan Najeriya, nasarorin gwamnatin Tinubu da shirye-shiryen jam’iyyar yayin neman wa’adin mulki na biyu a 2027.
Asali: Legit.ng


