Matashin Dan APC Ya Kama Sunan Buhari, Ya Fadi Rashin Kyautawar da Ya Yi wa Tinubu a 2023
- Alwan Hassan ya ce mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ne bisa ƙarfin siyasarsa.
- Matashin na APC ya zargi marigayi Muhammadu Buhari da rashin bai wa takarar Tinubu cikakken goyon baya a lokacin zaɓen
- Alwan Hassan ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da aka yi da shi kan yiwuwar sake zaɓen Shugaba Tinubu a shekarar 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Alwan Hassan, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ne duk da ƙalubale da dama.
Alwan Hassan ya yi zargin cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bai bai wa takarar Tinubu cikakken goyon baya ba a lokacin zaɓen.

Source: Facebook
Matashin na APC ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamban 2026 yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels tv.
Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan damar da Tinubu ke da ita ta samun wa’adi na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ya ce nasarar da Tinubu a 2023 ya samu ta samo asali ne musamman daga ƙarfinsa na siyasa, ba wai saboda cikakken goyon bayan Buhari da tsarin siyasarsa ba.
Ya yi magana kan goyon bayan Buhari
A yayin hirar, an tambayi Alwan Hassan ko Tinubu zai iya cin moriyar tsarin siyasa da tushen magoya bayan da tsohon shugaban ƙasa Buhari ya bari, musamman yayin da APC ke shirin sake fafatawa a zaɓen shugaban ƙasa.
Da yake amsa tambayar, Alwan Hassan ya nuna shakku kan ko Buhari ya bai wa Tinubu cikakken goyon bayan siyasarsa a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan
Tinubu ya kwantar da hankulan 'yan Najeriya, ya fadi shirinsa kan kawo karshen rashin tsaro
"Shin ya samu irin wannan goyon baya a 2023? Shin mun samu goyon bayan Buhari a 2023? Bari mu faɗi gaskiya, ba mu samu ba.” In ji shi.
Lokacin da aka tambaye shi ko yana nufin Tinubu ya lashe zaɓen 2023 ne da ƙarfinsa kawai, sai ya amsa da cewa haka ne.
Ya jaddada cewa Buhari bai fito fili ya goyi bayan burin Tinubu na zama shugaban ƙasa ba yadda ya kamata.
"Da ƙarfinsa ne. Buhari bai fito gaba ɗaya ya goyi bayan Tinubu ba.” In ji shi.
Ya zargi Buhari da rashin kamfen ga Tinubu
Ya ƙara da cewa Buhari bai taka rawar da ta dace wajen yaƙin neman zaɓen Tinubu ba a 2023, duk da cewa dukansu ’yan jam’iyyar APC ne.
A cewarsa, tsohon shugaban ƙasar bai fito fili ya nuna goyon baya ga Tinubu da kuma taimaka masa wajen neman ƙuri’un jama’a ba.
“Buhari bai yi abin da ya dace ba a 2023. Bai fito fili ya tsaya tare da mu da kuma Asiwaju ba a lokacin zaɓen. Asiwaju ya lashe wannan zaɓe ne duk da tarin ƙalubalen da ya fuskanta.”
Kalaman Alwan Hassan sun zo ne yayin da APC ke shirin tunkarar zaɓen 2027, inda Tinubu ke neman sake samun damar jagorantar ƙasar na wa’adi na biyu.

Source: Twitter
Amaechi ya ce ana kewar Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya ce ’yan Najeriya sun fara kewar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Amaechi ya bayyana cewa, a ra’ayinsa, rayuwa ta fi sauƙi a lokacin mulkin marigayi Buhari fiye da yadda take a ƙarƙashin gwamnatin APC mai ci yanzu.
Asali: Legit.ng

