‘Yar takara ta rabu da NDC, ta bi bayan APC da ta hakura da shiga zaben gwamna
- Stella Charles Archibong mai takarar mataimakiyar gwamna ta NDC a Cross River, ta watsar da neman mulki a jihar
- ‘Yar siyasar ta bayyana goyon bayanta ga Gwamna Bassey Otu na APC domin neman wa’adi na biyu a takarar 2027
- Ɗan takarar gwamnan NDC, John Odey, ya ce matakin ya ba shi mamaki, amma ya nemi masoya su kwantar da hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Cross River - NDC ta reshen jihar Cross River ta gamu da koma-baya gabanin zaɓen gwamna na 2027 kamar yadda ya faru da ita a wasu wurare.
Mai neman takarar kujerar mataimakiyar gwamna, Stella Charles Archibong, ta janye, wannan ya kawo wa tikitin jam’iyyar NDC gibi a jihar Cross River.
Stella Archibong ta sanar da ficewarta daga jam’iyyar ne cikin wata sanarwa da ta fitar a Calabar ranar Laraba kamar yadda Premium Times ta ce.

Kara karanta wannan
Matsaloli 10 da Sheikh Isa Pantami ya tsallake wajen zama ‘dan takarar gwamna a Gombe
‘Yar siyasar ta bayyana goyon bayanta ga Gwamna Bassey Otu, ta goyi bayan ya sake lashe zaɓen gwamnan jiha da za a yi a farkon shekarar badi.
Stella Archibong za ta taimaki APC a ƙarƙashin ƙungiyarta mai suna Back to South Movement.
Ta ce ta yanke wannan shawarar ne bayan shawarwari da dama da ta yi da dattawa, ’yan uwanta, al’ummar Kirista da kuma masu ruwa da tsaki a siyasa.
A jawabin da ta fitar a safiyar yau, Archibong ta bayyana cewa nauyin da ke kanta na yi wa Jihar Cross River hidima ya fi burinta na siyasa muhimmanci.
Saboda haka ne ta yanke shawarar mara wa tafarkin siyasar Gwamna Otu baya a 2027.
Ta ce:
“Nauyin da ke kaina na yi wa Jihar Cross River hidima ya fi buri na na kashin kai muhimmanci.”
Tsohuwar 'yar takarar ta yi wa NDC godiya
Haka kuma, ta nuna godiyarta ga shugaban NDC na jihar, Goddy Akwama, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar, John Odey wanda da suke tare.
‘Yar siyasar ta kuma yi godiya na musamman ga shugabannin jam’iyyar na ƙasa bisa damar da suka ba ta na yin takarar gwamna a ƙarƙashin NDC.
Ta nemi afuwar magoya bayanta da ka iya jin takaici sakamakon matakin da ta ɗauka, tare da gode masu bisa goyon baya da na’am da ita da suka yi.
Martanin ɗan takarar gwamnan NDC a Cross Rivers
Da yake mayar da martani, ɗan takarar gwamnan NDC ya ce matakin ya ba shi mamaki, amma ya buƙaci mutane su kwantar da hankalinsu.
Jaridar People Gazette ta ce a cikin wata sanarwa, Odey ya ce wannan lamari na buƙatar natsuwa, mutunta juna da kuma shugabanci na gari.
“Wannan lamari ya zo mana a matsayin abin mamaki. Ina ganin irin wannan lokaci na buƙatar natsuwa, dattako, mutunta juna da kuma shugabanci na gari.”
- John Odey
Odey ya ce yana mutunta Archibong sosai har da yaba wa irin gudummawar da ta bayar da kuma jajircewarta wajen ganin cigaban jiharsu.
Ya ƙara da cewa suna ci gaba da tattaunawa da shugabannin jam’iyyar da sauran waɗanda abin ya shafa domin fahimtar dalilan janyewarta.
Asali: Legit.ng
