"An Ci Amanata": Tsohon Gwamna Ya Koka bayan Gama Wahala da PDP
- Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ya riƙa ɗaukar nauyin tarukan PDP, hayar jiragen sama da biyan alawus ga mahalarta a lokacin da jam’iyyar ke fama da ƙarancin kuɗi
- Ya ce ya taimaka wa tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo bayan fitowarsa daga gidan yari, ciki har da samar masa da jirgin sama
- Kalu ya ce abin da ya samu a madadin gudunmawarsa shi ne durƙushewar kasuwancinsa, inda ya musanta cewa PDP ce ta ba shi damar zama gwamna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar mazaɓar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya zargi jam’iyyar PDP da juya masa baya.
Sanata Kalu ya ce PDP ta ci amanarsa duk da cewa ya ce ya kashe makudan kuɗaɗe wajen kafa jam’iyyar da kuma kula da ayyukanta.

Source: Facebook
Kalu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Arise TV a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamban 2026 inda ya ce ya ɗauki nauyin gudanar da tarukan jam’iyyar a lokacin da take fama da matsalar kuɗi.
Ya ce gudunmawar da ya bayar ta haɗa da biyan kuɗin hayar jiragen sama, alawus ga mahalarta taro da kuma samar da abinci a wuraren taruka.
Yadda ya taimaka wajen tafiyar da PDP
Sanatan ya bayyana cewa ya bayar da waɗannan gudunmawar ne saboda burinsa na ganin an kafa jam’iyyar siyasa mai ƙarfi wadda za ta taimaka wajen kawo ƙarshen mulkin soji a Najeriya.
A cewarsa, ya fara kashe kuɗaɗe wajen gina PDP tun kafin wasu manyan ’yan siyasa su shiga cikin bayar da tallafin kuɗi ga jam’iyyar.
“Ni ne nake ɗaukar nauyin tarukan, hayar jiragen sama, biyan alawus ga mutanen da suka zo, da kuma samar da abinci da sauran abubuwa. Wannan ita ce gaskiya.” In ji shi.
Kalu ya ƙara da cewa ya fara tallafa wa jam’iyyar da kuɗinsa tun kafin wasu manyan mutane su fara bayar da gudunmawarsu.
Kalu ya ce ya taimaka wa Obasanjo
Sanatan ya kuma bayyana cewa yana cikin mutanen da suka tallafa wa tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo bayan fitowarsa daga gidan yari.
Ya ce Obasanjo ya zauna a gidansa bayan an sake shi, yayin da shi kuma ya riƙa taimaka masa da kuɗi da kuma shirya masa jiragen sama domin zirga-zirgarsa.
“Na kawo kuɗin kafa jam’iyyar tun kafin manyan mutane kamar ku su fara kawo nasu tallafin. Na fara bayar da kuɗi da ɗaukar nauyi, kamar yadda na yi wa Shugaba Obasanjo lokacin da ya fito daga gidan yari.” In ji shi.
Ya ce PDP ta juya masa baya
Duk da irin gudunmawar da ya ce ya bayar, Kalu ya bayyana cewa yana jin jam’iyyar ta ci amanarsa, domin a maimakon ta yaba masa, sai ta juya masa baya.
Ya yi iƙirarin cewa sakamakon wannan rashin fahimta da jam’iyyar, kasuwancinsa ya fuskanci matsala.
Sai dai ya ƙi amincewa da ra’ayin cewa zama gwamnan Abia da ya yi wata alfarma ce da PDP ta saka masa saboda gudunmawar da ya bayar.
A cewarsa, da ya so, zai iya zama gwamna ta wata jam’iyyar siyasa daban, ba lallai sai ta PDP ba.
Kalu ya bayyana abin da ya ce ya samu a madadin gudunmawar da ya bayar da cewa:

Kara karanta wannan
Gwamna ya yi magana mai zafi kan harin da aka kai wa ayarin Peter Obi da Kwankwaso
“Abin da na samu a madadin haka shi ne lalacewar kasuwancina.”

Source: Facebook
Sanata Kalu ya hango nasarar Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Abia kuma sanatan da ke wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya kare manufofin sauye-sauyen tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu.
Sanata Kalu ya kuma yi hasashen cewa mai girma Tinubu zai lashe zaben shugaban kasa na 2027 da ake tunkara da gagarumar nasara.
Asali: Legit.ng

