Wata Sabuwa: Dalung Ya Hango Matsalar da Za Ta Iya Zama Hatsari ga ADC a Zaben 2027

Wata Sabuwa: Dalung Ya Hango Matsalar da Za Ta Iya Zama Hatsari ga ADC a Zaben 2027

  • Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya zargi sakataren ADC na ƙasa, Rauf Aregbesola, da naɗa kwamitocin riƙon ƙwarya a jihohi
  • Dalung ya ce naɗin ya zo ne yayin da ake jiran hukuncin Kotun Ƙoli kan takaddamar shugabancin jam’iyyar
  • Ya bukaci ADC ta dakatar da rantsar da kwamitocin da aka shirya yi domin kada hakan ya jefa shigar jam’iyyar zaɓen 2027 cikin haɗari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Wani jigo a jam’iyyar ADC, Solomon Dalung, ya zargi sakataren jam’iyyar na ƙasa, Rauf Aregbesola, da naɗa kwamitocin riƙon ƙwarya a jihohin Najeriya ba tare da bin tsarin da ya dace ba.

Dalung, wanda tsohon Ministan Matasa da Ci Gaban Wasanni ne, ya ce matakin na iya raunana shari’ar da jam’iyyar ke yi a Kotun Ƙoli tare da jefa shigarta zaɓen 2027 cikin haɗari.

Kara karanta wannan

"Ku ce ni da Kwankwaso mun gaza"; Peter Obi ya dauki muhimmin alkawari ga 'yan Najeriya

Solomon Dalung ya hango kuskuren ADC
Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung Hoto: Barr Solomon Dalung
Source: Facebook

Ya bayyana zargin ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata, 10 ga watan Nuwamban 2026.

Tsohon ministan ya yi zargin cewa an rarraba wasiƙun naɗin mambobin kwamitocin riƙon ƙwarya, waɗanda ake zargin Aregbesola ya sanya wa hannu, domin su kula da harkokin jam’iyyar a faɗin ƙasar.

Ya ce matakin na iya shafar shari’ar ADC

Dalung ya nuna damuwa kan yadda shugabancin jam’iyyar ke ci gaba da yanke muhimman shawarwari duk da cewa akwai ƙara da ke gaban Kotun Ƙoli.

“A yammacin yau, ina isar da saƙo mai ƙarfi ga shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress a Najeriya. Da alama jam’iyyar ba ta koyi darasi daga yawan ƙararrakin shari’a da ke gabanta ba.
“Mun wayi gari a yau shafukan sada zumunta cike da wasiƙun naɗin mambobin kwamitocin riƙon ƙwarya na jihohi 36, waɗanda sakataren jam’iyyar na ƙasa ya sanya wa hannu.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kwantar da hankulan 'yan Najeriya, ya fadi shirinsa kan kawo karshen rashin tsaro

Ya kuma yi zargin cewa waɗanda aka naɗa sun haɗa da mutanen da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta cire daga muƙamansu, yayin da ƙalubalantar hukuncin kotun ke jiran sauraro a Kotun Ƙoli.

Ya zargi shugabancin ADC da raina tsarin shari’a

Dalung ya bayyana matakin naɗin a matsayin rashin bin ƙa’idojin doka, yana mai zargin shugabancin ADC da ƙoƙarin riga-kafin hukuncin da Kotun Ƙoli za ta yanke.

"Wannan mataki na jam’iyyar an ɗauke shi ne domin raunana martabar bangaren shari’a da kuma ƙoƙarin riga-kafin hukuncin da mai girma alƙalai za su yanke kan batun da ke gabansu a Kotun Ƙoli.
“Wannan abu ba abin karɓuwa ba ne ga ’yan Najeriya masu tunani nagari da masu kishin bin doka da dimokuraɗiyya. A matsayina na tsohon minista a fannin shari’a kuma lauya mai cancantar zuwa Kotun Ƙoli, ba zan goyi bayan ADC wajen lalata tsarin shari’a ba.” In ji shi.

Dalung ya bukaci a dakatar da rantsar da su

Dalung ya bukaci shugabancin ADC da ya dakatar da shirin rantsar da mambobin kwamitocin riƙon ƙwarya, wanda aka tsara gudanarwa ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamban 2026.

Kara karanta wannan

Tsohon abokin takarar Buhari ya bayyana dalilin kin karbar tayin mukamin da Tinubu ya yi masa

Ya ce ya kamata jam’iyyar ta jira Kotun Ƙoli ta yanke hukunci kan ƙarar da ke gabanta kafin ta ɗauki irin waɗannan matakai.

Tsohon ministan ya yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da rantsar da kwamitocin, hakan na iya ƙara dagula matsalar shari’ar jam’iyyar da kuma kawo cikas ga shigarta zaɓen 2027.

“Idan jam’iyyar ta ci gaba da rantsar da waɗannan mutane, sakamakon hakan a bayyane yake. Ma’anarsa ita ce ADC ba ta da niyyar shiga zaɓen 2027.” In ji shi.
Dalung ya yi magana kan rikicin ADC
Solomon Dalung zaune a ofis Hoto: Barr. Solomon Dalung
Source: Getty Images

Dalung ya yi zargi kan 'yan majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan harkokin matasa da wasanni, Solomon Dalung ya yi zargin cewa ‘yan majalisa sun nemi cin hanci daga wajen shi.

Barista Solomon Dalung ya ce ‘yan majalisar Najeriyan sun bukaci ya biya cin hanci na N200m lokacin da ya nemi kare kasafin kudin ma’aikatarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng