Babban Mai Adawa da Pantami Ya Nemi Afuwa, Ya Ce 'Gombe sai Malam'

Babban Mai Adawa da Pantami Ya Nemi Afuwa, Ya Ce 'Gombe sai Malam'

  • Ahmed Shuaibu Gara Gombe ya nemi afuwar Farfesa Isa Ali Pantami kan kalaman da ya taɓa yi masa a baya, yana mai cewa wasu daga cikinsu sun fito ne sakamakon fushi
  • Gara Gombe ya ce bayan nazarin siyasar jihar Gombe da kuma tarihin aikin Pantami, ya gamsu cewa tsohon ministan zai iya jagorantar jihar zuwa ga ci gaba
  • Tsohon mai adawa da Pantami ya bayyana cewa a wannan karon zai yi aiki tare da shi, duk da cewa ba ya cikin kowace jam'iyyar siyasa, yana mai cewa zai goyi bayan shirin Pantami na 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe – Ahmed Shuaibu Gara Gombe, wanda a baya ya kasance mai tsananin adawa da Farfesa Isa Ali Pantami, ya sauya matsayinsa tare da bayyana aniyarsa ta mara masa baya a zaben gwamnan Gombe na 2027.

Kara karanta wannan

Labaran bogi da suka rika yawo a kafafen sada zumunta a makonnin nan

Gara Gombe ya nemi afuwar Pantami kan wasu kalamai da ya yi game da shi a baya, yana mai cewa ya san sun ɓata masa suna kuma wasu daga cikinsu sun samo asali ne daga fushi.

Gara Gombe da Sheikh Isa Ali Pantami
Gara Gombe a hagu da Sheikh Isa Ali Pantami a dama. Hoto: Gara Gombe|Abba Sani Pantami
Source: Facebook

A wata budaddiyar wasika da ya rubuta wa Pantami a Facebook a ranar Laraba, 7 ga Oktoba, Gara Gombe ya ce duk da cewa ba duk abin da ya faɗa a baya ba ne ba daidai ba, ya nemi gafarar duk wani abu da ya cutar da shi.

Gara Gombe ya gamsu da Pantami

Gara Gombe ya ce ya sake duba yanayin siyasar Gombe tare da nazarin tarihin karatun Pantami da ayyukansa, inda ya ce hakan ya tabbatar masa da cewa Pantami na da abin da ake buƙata domin jagorantar jihar.

Ya ce ya kuma saurari hirarrakin Pantami daban-daban, musamman yadda yake magana kan tsare-tsarensa ga al'ummar Gombe.

Gara Gombe ya ce:

“Na sake nazarin siyasar jihar Gombe. Na kuma nazarci tarihin aikinka, kuma na gamsu cewa kana da abin da ake buƙata domin jagorantar jiharmu da mayar da ita kan turbar ci gaba da bunƙasa.”

Kara karanta wannan

2027: Minista ya dage yana yi wa Tinubu aiki domin APC ta yi nasara a jihohi 5

Me Gara Gombe ke so a Gombe?

Gara Gombe ya ce al'ummar Gombe na buƙatar gwamnati da za ta kawo wa jama'a abubuwa, ba wadda za ta karɓe masu ba.

Ya kuma ce ana buƙatar shugabanci cikin tausayi da mutunta dattawa da jama'a, maimakon tsarin mulki da yake amfani da tilas.

Ya yi nuni da wata magana da ya ce an taɓa yi wa wani dattijo mai kusan shekaru 80 a bainar jama'a, yana mai cewa al'ummar jihar ba za su ƙara amincewa da irin wannan salon shugabanci ba.

Ya ce zai yi aiki da Pantami

Gara Gombe ya bayyana cewa a wannan karon Pantami zai samu goyon bayansa, yana mai cewa zai yi aiki tare da shi domin cimma manufofinsa.

Ya ce:

“A wannan karon kana da wani kwamanda. Ƙungiyoyin da suka yi ƙoƙarin kawo ƙarshen tafiyarka sun yi ƙoƙari kuma har yanzu suna ƙoƙari. Abin takaici a gare su, lokaci ya kure.”

Gara Gombe ya kuma ce ba ya cikin kowace jam'iyyar siyasa kuma bai taɓa kasancewa ɗan wata jam'iyya ba, duk da cewa ya taɓa aiki tare da ‘yan siyasa.

Kara karanta wannan

'Su suke kawo kansu': Pantami kan 'yan TikTok da ke barinsa zuwa Jamilu

Ya ce hakan ne ya sa ya kafa Gombe First Project, wanda yake amfani da ita wajen bibiya da kuma ƙarfafa ‘yan takarar da ya yi imanin suna da abin da za su iya bayarwa ga jihar.

Sheikh Pantami a Gombe
Dan takarar PDP, Sheikh Isa Ali Pantami. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Gara ya yi wa Pantami alkawari

Gara Gombe ya ce zai yi aiki tare da Pantami kuma ya mara masa baya bisa tsarin tafiyar jam'iyyarsa, amma ba tare da ya zama ɗan jam'iyyar ba.

Ya ce:

“Saboda haka, zan yi aiki tare da kai kuma domin kai bisa tsarin taswirar tafiyar jam'iyyarka, amma ba a matsayina na ɗan jam'iyyar ba.”

A ƙarshen wasikar, Gara Gombe ya yi addu'ar Allah Ya kare Pantami tare da fatan ganin an rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar Gombe a ranar 29 ga Mayu, 2027.

'Yan APC sun koma PDP a Gombe

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu jiga-jigan siyasa da magoya bayansu daga ƙaramar hukumar Yamaltu/Deba sun fice daga jam'iyyar APC zuwa PDP, inda suka bayyana goyon bayansu ga Pantami a zaben 2027.

Mutanen da suka sauya sheƙar sun haɗa da tsofaffin sojoji, tsofaffin ma'aikatan gwamnati, ‘yan siyasa da kuma wasu masu tasiri a matakin ƙasa, waɗanda aka karɓe su a PDP tare da tsohon gwamnan Gombe, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, da Pantami.

A cewar bayanin da aka fitar, waɗanda suka sauya sheƙar sun yi alƙawarin amfani da hanyoyin sadarwarsu da tsarin da suke da shi a matakin ƙasa domin tallafa wa ‘yan takarar PDP a Yamaltu/Deba a zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng