Magana Ta Fito: An Ji Dalilin da Ya Sa Malaman Musulunci Suka Goyi Bayan Tinubu a 2027

Magana Ta Fito: An Ji Dalilin da Ya Sa Malaman Musulunci Suka Goyi Bayan Tinubu a 2027

  • Sama da malaman Musulunci 500 daga jihohin Arewa 19 da Abuja ne suka bayyana goyon bayansu ga sake zaben Bola Tinubu a 2027
  • Ministan Gidaje, Muttaka Rabe Darma ya fito ya yi karin haske kan dalilin malaman na daukar wannan mataki
  • Taron malaman ya yaba da inganta tsaro a Kaduna, Katsina da Sokoto, tare da neman ƙarin aiki a Neja da Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja, Nigeria - Ministan Gidaje da Raya Birane, Muttaka Darma Rabe, ya fito ya yi bayani kan goyon bayan malaman Musulunci ga tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Tun farko dai an bayyana cewa malaman Musulunci 500 daga jihohin Arewa 19 da Abuja sun amince da sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya yi shekara takwas a kan mulki.

Darma.
Ministan harkokin gidaje da raya birane, Muttaka Rabe Darma Hoto: Mustapha S. Galadima
Source: Facebook

Tribune Nigeria ta ce malaman sun bayyana hakan ne a ƙarshen wani taron dabarun siyasa da aka gudanar a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, ranar Asabar, inda aka tattauna kan abubuwan da gwamnatin Tinubu ta cimma a Arewa.

Kara karanta wannan

Tawagar gwamnatin tarayya ta sauka a Kano don ta'aziyyar dattijon APC

Taron ya samu halartar gwamnoni shida na Arewa, ciki har da Uba Sani na Kaduna, Dikko Radda na Katsina, Mala Buni na Yobe da Umar Namadi na Jigawa.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Kabir Ibrahim Masari, da wasu manyan jami’an gwamnati sun halarci taron.

Malamai sun goyi bayan Tinubu

Da yake karanta ƙudurin taron, Rabe Darma ya ce an gayyaci malaman Musulunci, masu wa’azi da masana daga jihohin Arewa 19 da Abuja domin tattauna ci gaban da yankin ya samu tun bayan hawar gwamnatin Tinubu.

“Fiye da malaman Musulunci, masu wa’azi da limamai 500 daga jihohin Arewa 19 da Abuja sun kada ƙuri’ar amincewa da Shugaba Bola Tinubu tare da yin kira da a goyi bayan sake zabensa a 2027.”

Ministan ya ce taron malaman Musulunci ya yi nazari kan ayyukan gwamnatin Tinubu, inda ya gano cewa gwamnati na samun ci gaba a fannonin tsaro, ababen more rayuwa da raya Arewa.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadr gwamnati da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Dalilin malamai na goyon bayan Tinubu

A cewar Rabe, taron ya nuna cewa an samu sauƙin matsalolin tsaro a Kaduna, Katsina da Sokoto, duk da cewa har yanzu akwai buƙatar ƙarin aiki a jihohin Niger da Zamfara.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027 akwai kallo, masu ruwa da tsakin PDP, ADC sun goyi bayan Tinubu

Taron ya kuma mayar da hankali kan gyaran babbar hanyar Kano zuwa Kaduna, inda malaman suka bayyana ta a matsayin muhimmiyar hanya ga harkokin kasuwanci da tattalin arzikin yankin.

Ya ce malaman sun duba ci gaba da aka samu, bisa haka suka ga ya dace su karwa Tinubu baya a karo ma biyu.

Tinubu zai iya kayar da Kwankwaso a Kano

Kun ji cewa Hon. Abdulmumin Jibrin ya ce Shugaba Bola Tinubu zai kayar da Rabiu Kwankwaso a Kano a zaben shugaban kasa na 2027.

Dan majalisar, wanda a baya ya kasance abokin siyasar Kwankwaso amma yanzu yake APC mai mulki, ya ce sanin tsarin siyasar Kwankwaso zai taimaka musu wajenNsamun galaba a kansa.

Jibrin ya amince Kwankwaso na da karfin fada aji a Kano, amma ya ce kasancewarsa dan takarar mataimakin shugaban kasa zai sauya lamarin

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262