'Minista Ya Fi Ka Gaskiya': An Bukaci El Rufai Ya ba Kudancin Kaduna Hakuri
- Kungiyar Middle Belt Forum ta goyi bayan Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa kan rigimarsa da Nasir El-Rufai
- Sakataren yaɗa labaran ƙungiyar, Luka Binniyat, ya ce MBF na magana ne a matsayin shaidun abubuwan da suka faru a mulkin El-Rufai
- Kungiyar ta buƙaci gudanar da bincike kan zargin kashe-kashe, biyan kuɗi ga ’yan bindiga da rushe-rushe da suka faru a mulkinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Kungiyar Middle Belt Forum, MBF, ta goyi bayan Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, inda ta ce Nasir El-Rufai ne ya kamata ya nemi gafara.
Kungiyar ta ce tsohon Gwamnan Kaduna ya kamata ya nemi gafarar al’ummar Kudancin Kaduna kan abubuwan da suka faru a lokacin mulkinsa.

Source: Facebook
Sakataren yaɗa labaran ƙungiyar na ƙasa, Luka Binniyat, ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Ministan tsaro ya sa Majalisar kolin harkokin Musulunci ta dauki zafi a shari’ar El Rufai
An bukaci El-Rufai ya nemi afuwa
Binniyat yana mayar da martani ne kan buƙatar iyalan El-Rufai ga Ministan Tsaro, inda suka nemi ya nemi gafara saboda kalaman da ya yi kan tsohon gwamnan.
Binniyat ya ce ƙungiyar ba ta magana ne a madadin Janar Musa ba, sai dai a matsayin shaidun abubuwan da suka faru a Kaduna lokacin mulkin El-Rufai.
Ya ce:
“Janar Musa ba zai nemi gafara ba; maimakon haka, El-Rufai ne ya kamata ya nemi gafara ga mutanen Kudancin Kaduna.
“Idan iyalan suka dage kan kai Janar Musa kotu, muna da isassun hujjojin da za mu gabatar a kan El-Rufai.”

Source: Twitter
'Hakkin Kudancin Kaduna, Middle Belt kan El-Rufai'
Kakakin MBF ya kuma bayyana cewa ƙungiyar ba ta zama kakakin Janar Musa ba, tana magana ne a matsayin shaidun abubuwan da suka faru a Kaduna.
Ya ce Kudancin Kaduna na cikin yankin Middle Belt, don haka ƙungiyar na da damar magana kan abubuwan da suka shafi yankin.

Kara karanta wannan
'Neman fitina yake yi': Gwamnatin Benue ta yi martani mai zafi bayan jifan Peter Obi
Kungiyar ta yi zargin cewa abin da ya sauya a ƙarƙashin Nasir El-Rufai shi ne kai wa al’ummomin karkara masu rauni hari da gangan.
A cewar MBF, ayyuka da kalaman gwamnatin El-Rufai sun ƙarfafa irin wannan yanayi, wanda ta ce ya jefa al’ummomin yankin cikin wahala.
Kungiyar ta bayyana goyon bayanta ga Musa kan kalaman da ya yi, tana mai cewa suna da alaƙa da tarihin radadin da al’ummar Middle Belt ta Kaduna suka fuskanta, cewar Daily Post.
MBF ta ce akwai zargin cewa tsohon gwamnatin El-Rufai ta taka rawa wajen kisan mutane da dama a yankin Middle Belt na Kaduna da sauran sassan jihar.
Kungiyar ta ce:
“MBF na ganin ya kamata a gurfanar da El-Rufai kan laifukan cin zarafin bil’adama tare da miƙa shi ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, ICC.”
El-Rufai, ministan tsaro: JNI, CAN sun tsoma baki
An ji cewa shugabannin addinai Musulmi da Kirista a Kudancin Kaduna sun yi kira ga zaman lafiya, yayin da Nasir El-Rufai ya nemi N10bn.
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya nemi Ministan Tsaro, Christopher Musa ya ba shi hakuri, tare da biyan N10bn saboda zargin bata masa suna.
Kungiyar JNI da CAN sun bukaci jama'a su guji mayar da rikicin zuwa na addini ko kabilanci, yayin da wata kungiya ta goyi bayan Musa.
Asali: Legit.ng