Dan Kasuwa Ya Rasa Ransa yayin Kara Masa Girman Mazakuta a Asibiti
- Wani ɗan kasuwar dan Najeriya da ke rayuwa a Birtaniya ya mutu bayan wani aikin ƙara girman azzakari a Thailand
- Mutumin ya mutu ne a watan Maris, bayan an yi masa allurar mililita 40 na hyaluronic acid da lidocaine a wani asibiti dake Bangkok
- Majiyoyi sun ce ya fara jin ciwon ƙirji tare da suma sau biyu yayin da yake yin tausa tare da matarsa, Danielle Simba Allen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bangkok, Thailand - Wani dan Najeriya da ke rayuwa a Birtaniya, Igho Ubiribo ya mutu bayan wani aikin ƙara girman azzakari a Thailand.
Mutumin ya mutu ne a watan Maris, bayan an yi masa allurar mililita 40 na hyaluronic acid da lidocaine a wani asibiti dake Bangkok.

Source: Facebook
Yadda ani ya mutu kan aikin mazakuta
Majiyoyi daga Vanguard ya ce fara jin ciwon ƙirji tare da suma sau biyu yayin da yake yin tausa tare da matarsa, Danielle Simba Allen.
An garzaya da shi asibitin Sukhumvit da motar asibiti, inda likitoci suka gano cewa yana fama da toshewar wata jijiyar jini a huhu.
Daga bisani ya sake suma kafin a gudanar da gwajin CT da likitoci suka ba da shawara domin gano matsalar da ke damunsa sosai.
Likitoci sun yi ƙoƙarin farfaɗo da shi na tsawon sama da mintuna 100, amma ya rasu a farkon safiyar ranar 6 ga Maris.
Binciken gawarsa da aka gudanar a Birtaniya ya gano cewa ƙwayoyin halitta da ke huhunsa sun yi daidai da hyaluronic acid da aka yi amfani da shi wajen allurar.
Wannan binciken ya ƙara ƙarfafa zargin cewa Ubiribo ya mutu ne sakamakon wasu matsaloli da sua shafi toshewar jini a huhu bayan aikin allurar.
Mai binciken mutuwar, Jean Harkin, ta tabbatar da cewa Ubiribo ya mutu “sakamakon aikin gyaran jiki da aka yi a ƙasar waje”, cewar Punch.
An rubuta dalilin mutuwarsa ne bayan alluran da aka yi masa, wanda ya samo asali daga sinadarin allurar 'hyaluronic' da aka yi masa a azzakari.
Rahotanni sun ce Ubiribo, wanda ke da kusan mabiya 185,000 a Instagram, an yi masa jana’iza a London cikin watan Mayu.

Source: Instagram
Davido, manyan mutane sun halarci jana'izarsa
An bayyana cewa fitaccen mawakin Najeriya, Davido, da wasu manyan mutane sun halarci jana’izar marigayin a London.
Kwararrun likitocin lafiya sun taɓa bayyana damuwarsu kan ayyukan amfani da filler wajen ƙara girman azzakari saboda haɗarin da suke iya haifarwa.
Farfesa Vaibhav Modgil, ƙwararren likitan andrology na NHS kuma likitan tiyata, ya ce irin wannan aiki na iya haifar da mummunan sakamako ga marasa lafiya.
An yi dashen mazakuta a Vietnam
An ji cewa likitoci a ƙasar Vietnam sun yi nasarar gudanar da aikin dasa mazakuta ga wani mutum mai shekaru 43 ta amfani da sashen jikin wani da ya mutu.
An gudanar da aikin ne bayan an cire wani ɓangare na mazakutar mutumin shekaru huɗu da suka gabata, kuma likitoci sun tabbatar ya dace a aikin.
Asibitin ya ce maras lafiyar na ci gaba da samun sauƙi, yayin da ake bibiyar yadda sabon sashen jikin zai ci gaba da aiki a nan gaba.
Asali: Legit.ng

