Malamin Addini Ya Samo Hanyar Kifar da Tinubu ga 'Yan Adawa a Zaben 2027

Malamin Addini Ya Samo Hanyar Kifar da Tinubu ga 'Yan Adawa a Zaben 2027

  • Primate Ayodele ya ce Tinubu ya riga ya fara shirin neman wa’adi na biyu, don haka ‘yan adawa su gaggauta hada kawance
  • Ya yi zargin cewa akwai ‘yan takarar shugaban kasa biyu a bangaren adawa da aka shirya amfani da su wajen tarwatsa kawancen
  • Malamin addinin ya ba da shawarar jam’iyyun adawa hudu ko biyar masu ra’ayi iri daya su hada karfi domin kalubalantar Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Primate Elijah Ayodele, shugaban INRI Evangelical Spiritual Church da ke Legas, ya gargadi jam’iyyun adawa kan zaben 2027.

Primate Ayodele ya yi gargadin cewa ba za su iya samun nasara a zaben shugaban kasa na 2027 ba idan ba su hada kai ba.

Primate Ayodele ya ja kunnen 'yan adawa
Shugaban cocin INRI, Primate Elijah Babatunde Ayodele Hoto: Primate Elijah Babatunde Ayodele
Source: Facebook

Legit.ng ta ce Ayodele ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 25 ga Agusta, 2026, cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin, ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

"Ka shirya barin Aso Villa"; Melaye ya fadi dabarar ADC ta kifar da Tinubu a 2027

Ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya riga ya fara shiri mai karfi domin neman wa’adi na biyu, kuma hakan ya sa jam’iyyun adawa ke bukatar daukar matakin gaggawa idan suna son kalubalantar shi.

Ayodele ya gargadi 'yan adawa

Malamin ya yi zargin cewa Tinubu ya riga ya yi hasashen yiwuwar jam’iyyun adawa su hada kawance domin tunkarar sa a zaben 2027.

Ya kuma yi ikirarin cewa an shirya amfani da wasu mutane daga cikin ‘yan adawa domin tarwatsa duk wani kawance da aka kafa.

“Tinubu zai kafa nasa kawancen a cikinsu ta hanyar amfani da ‘yan leken asiri. Akwai ‘yan takarar shugaban kasa biyu a bangaren adawa da aka riga aka sasanta da su domin su tarwatsa kawancen,” in ji shi.

Saboda haka, Ayodele ya shawarci shugabannin jam’iyyun adawa da su yi taka-tsantsan wajen zabar jam’iyyun da za su shiga kawancen.

Wace shawara Primate Ayodele ya ba 'yan adawa?

Kara karanta wannan

Amaechi: Mataimakin Atiku ya bukaci 'yan Najeriya kada su zabi ADC, an ji dalili

Ayodele ya ce bai kamata jam’iyyun adawa su bude kofa ga kowace jam’iyya ba, sai dai su zabi jam’iyyu masu ra’ayi da manufofi masu kusanci.

Ya ba da shawarar cewa jam’iyyu hudu ko biyar ne kawai su hada karfi domin samar da kawance mai karfi.

A cewarsa, yawan jam’iyyun da ke cikin kawancen ba shi ne babban abin da zai tabbatar da nasara ba, illa dai kasancewar shugabanninsu suna da manufa daya.

“Ba kowace jam’iyya ce za ta shiga kawancen ba. Su hada jam’iyyu mafiya kyau su kafa kawance mai karfi. Jam’iyyu hudu ko biyar kawai su hada kai, kuma dole su fahimci manufofinsu.” In ji shi

Ayodele ya samo mafita ga 'yan adawa

Primate Ayodele ya jaddada cewa hadin kan ‘yan adawa shi ne hanya mafi muhimmanci da za ta ba su damar kalubalantar Tinubu a zaben 2027.

Ya ce Tinubu ya riga ya fara shirin tunkarar zaben, don haka ‘yan adawa ba za su samu damar kayar da shi ba idan suka ci gaba da fafatawa a tsakaninsu.

“Tinubu ya shirya tsaf domin wa’adi na biyu kuma ya riga ya wuce kowa. Abin da suke bukata yanzu shi ne su kafa kawance idan suna son lashe wannan zabe. Wannan ita ce hanya mafi sauki,” in ji Ayodele.

Kara karanta wannan

Minista ya fasa kwai, an ji yadda ake shirin ƙarawa Atiku 'hawan jini' kafin zaben 2027

Gargadin nasa ya zo ne yayin da ake kara samun tattaunawa tsakanin jam’iyyun adawa da ‘yan siyasa daban-daban kan yiwuwar kafa tafiya daya domin kalubalantar jam’iyyar APC a zaben 2027.

Shugaban kasa Bola Tinubu na neman wa'adi na biyu a mulki
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Peter Obi ya kalubalanci Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewaɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya kalubalanci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya fito gaban ‘yan Najeriya ya rika masu bayani kai tsaye.

Peter Obi ya bukaci Tinubu, wanda shi ne ɗan takarar jam’iyyar APC mai mulki, da kada ya dogara da wakilai ko ‘yan siyasa wajen neman ƙuri’un jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng