Ta Tabbata, Jagoran Addinin Kasar Musulunci ta Iran Yana Nan a Raye
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ce yana ganin har yanzu jagoran addinin kasar musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei, yana raye
- Shugaba Trump ya ce Khamenei ya samu munanan raunuka a bangaren hagu na jikinsa a hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai
- Shugaban Amurkan ya sake cewa matsin lambar soji da na tattalin arziki na kai Iran ga babbar rashin nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana ganin jagoran addinin Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei yana nan a raye, bai mutu ba.
Shugaba Trump ya ce Khmenei, wanda ba a gan shi a bainar jama'a ba tun bayan da ya karbi ragamar mulki bayan kashe mahaifinsa, Ali Khamenei a watan Fabrairu, 2026, yana raye amma ya samu raunika.

Source: Getty Images
Mojtaba Khamenei yana raye
Tashar Al-Jzeera ta ruwaito cewa Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da mai gabatar da shirin rediyon masu ra'ayin mazan jiya, Glenn Beck.
“Ba na tunanin ya mutu. Ya samu mummunan rauni sosai a bangaren hagu na jikinsa, hannu, kafa, komai. Ya samu munanan raunuka sosai. Amma ba na tunanin ya mutu,” in ji Trump.
Khamenei ya daina fitowa fili
A hukumance, Mojtaba Khamenei na ci gaba da jagorantar Iran yayin da Amurka da Isra’ila ke kai hare-hare kan kasar.
Sai dai rashin fitowarsa fili da kuma karuwar tasirin wasu manyan jami'an Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ya haifar da rade-radin cewa ko dai ya mutu ko kuma ba ya da cikakken iko a kan harkokin mulkin kasar.
An kashe mahaifinsa ne a wani harin bam da aka kai a farkon farmakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya
Trump ya yi alkawarin nasara
Trump, wanda ya sha bayyana cewa Amurka ta yi nasara a kan Iran, ya sake cewa matsin lambar soji da tattalin arziki da ya dauka kan kasar musuluncin suna aiki.
Sai dai har yanzu bai samu bude Mashigar Hormuz gaba daya ba, kuma Iran ba ta mika makamanta ko kayan nukiliyarta ba.
“Wadannan abubuwa suna tafiya ne zuwa babbar nasara. Za mu samu babbar nasara a nan nan ba da jimawa ba,” in ji Trump.

Source: Twitter
Trump ya kuma dage kan cewa Mashigar Hormuz, inda sojojin Iran suka kawo cikas tare da takaita zirga-zirgar jiragen ruwa, a zahiri a bude take gaba daya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Amurka ta kara jibgawa Iran takunkumi
A wani labarin, kun ji cewa Amurka ta ƙaddamar da wani sabon shirin matsin tattalin arziki kan Iran, tare da shirin katse hanyoyin samun kuɗin gwamnatin kasar ta Musulunci.
Ministan Baitul Malin Amurka, Scott Bessent, ya bayyana cewa sabon shirin zai shafi dukkan manyan hanyoyin samun kuɗin Iran, ciki har da fannin man fetur.
Ya bayyana cewa ƙasashe da kamfanonin da ke taimakawa wajen sayar da man Iran ko sauƙaƙa hanyoyin samun kuɗin za su iya fuskantar takunkumin Amurka.
Asali: Legit.ng
