MURIC: Kungiyar Musulunci Ta Takalo Ministar da Ta Hana Auren Marayu 100 a Neja

MURIC: Kungiyar Musulunci Ta Takalo Ministar da Ta Hana Auren Marayu 100 a Neja

  • Kungiya mai fafutukar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta yi martani ga ministar harkokin mata kan dakatar da auren marayu
  • Shugaban kungiyar na jihar Kano, alam Hassan Sani Indabawa ne ya yi martanin a jiya Alhamis, 16 ga watan Mayu
  • Shugaban majalisar dokokin jihar Neja, Abdulmalik Sarkindaji ne ya dauki nauyin auren marayu 100 amma ministar ta hana

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kungiya mai fafutukar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta yi martani ga ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye kan auren marayu 100 a jihar Neja.

MURIC NIG
MURIC ta ce auren marayu 100 a Neja bai saba ka'ida ba. Hoto: Muric Muslim-Rights/ Federal Ministry of Women Affairs
Asali: Facebook

Kungiyar ta yi kira ga ministar harkokin ta janye korafin da ta rubuta ga shugaban rundunar yan sandan Najeriya.

Kara karanta wannan

Niger: Ministar Tinubu ta yi amai ta lashe, ta dauki mataki kan aurar da mata 100

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa shugaban MURIC na jihar Kano, Malam Hassan Sani Indabawa ne ya yi kiran a jiya Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda minista ta hana auren marayu a Neja

Shugaban ya ce tunda kakakin majalisar jihar Neja, Abdulmalik Sarkindaji ne ya dauki nauyin auren bai kamata da saka baki ba.

Ana dai shirin daura auren ne a ranar Juma'a 24 ga watan Mayu sai aka ji ministan ta shigar da korafi domin takawa yunkurin burki.

A ranar Litinin da ta gabata ne ministan ta shigar da lamarin kotu domin hana shugaban majalisar gudanar da wannan auren.

Auren marayu: Matsayar shugaban MURIC ta Kano

Shuagan MURIC na reshen jihar Kano ya ce matakin da ministar ta dauka ya yi tsauri sosai kasancewar lamarin bai shafe ta ba.

Kara karanta wannan

Niger: Kotu ta raba gardamar ka-ce-na-ce game da aurar da mata marayu 100

Ya kuma kara cewa matakin da ta dauka ya nuna cewa ba ta da masaniya kan al'adun mutanen Arewacin Najeriya, rahoton Nigerian Bulletin.

Rawar da midiya ta taka kan lamarin

Malam Hassan Sani ya tabbatar da cewa matakin ya yi kokarin bata shugaban majalisar a idon masu amfani da kafafen sadarwa.

Shugaban ya ce kakakin majalisar ya yi yunkurin aikin ne tsakaninsa da Allah domin tallafawa marayun su 100.

A karshe yace ministar ta yi gaggawar janje kalaman ta domin lamarin auren babu tilastawa a ciki kuma bai saba doka ba.

MURIC ta goyi bayan Sheikh Gumi

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Ahmad Gumi ya caccaki ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike a kan karban bakuncin jakadan Isra'ila a ofishinsa.

A bidiyo mai tsawon mintuna 14 da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya bayyana Wike a matsayin shaidani daga baya kuma MURIC ta goyi bayan Gumi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel