An Kama Mutune 5 Kan Kisar Dan Sanata Kabiru Gaya Mai Wakiltar Kano, An Samu Karin Haske Kan Dalilin Kisarsa

An Kama Mutune 5 Kan Kisar Dan Sanata Kabiru Gaya Mai Wakiltar Kano, An Samu Karin Haske Kan Dalilin Kisarsa

  • Rundunar yan sandan Najeriya reshen birnin tarayya Abuja ta tabbatar da kama mutum biyar da ake zargi da hannu a kisar Sadiq Gaya, dan Sanata Kabiru Gaya
  • Josephine Adeh, mai magana da yawun rundunar yan sandan na Abuja ta ce wadanda ake zargin suna tsare kuma za a yi karin bayani da zarar bincike ya kammala
  • Wata majiya kwakwara ta bayyana cewa wani abokin Sadiq Gaya ne ya kitsa kisarsa saboda Naira miliyan 3.5

Abuja - Jami'an yan sandan Najeriya, reshen birnin tarayya Abuja sun kama mutane biyar da ake zargi da hannu kan kisar Sadiq Gaya, dan dan majalisar Kano, Sanata Kabiru Gaya a Abuja.

Kwarararn majiyoyi sun tabbatar wa wakilin The Punch cewa wani abokin Sadiq ne ya kitsa yadda za a kashe shi saboda N3.5m.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Za ta Kirkiro Bankuna na Musamman Domin Matasan Najeriya

Kabiru Gaya
An Kama Mutune 5 Kan Kisar Dan Sanata Kabiru Gaya Mai Wakiltar Kano, Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mahaifin marigayin, sanata mai wakiltan Kano ta Kudu, Gaya, dan shekara 70, sanata ne tun shekarar 2007, kuma a yanzu shine ciyaman na kwamitin INEC a majalisa.

Yan sanda sun tabbatar da kama wadanda ake zargi

Mai magana da yawun yan sandan Najeriya, Josephine Adeh, ta tabbatar da lamarin, ta ce an kama mutane biyar kan kisar, kuma suna hannun yan sandan ana cigaba da bincike.

Adeh ta ce:

"An kama mutum biyar da ake zargi da kisar, kuma ana cigaba da bincike. Idan an kammala za a sanar da sakamakon binciken."

Marigayin, Sadiq, lauya ne kuma ma'aikaci ne a hukumar kula da kadarorin Najeriya.

Allah Ya Yiwa Dan Sanata Kabiru Gaya Rasuwa a FCT Abuja

Tun da farko, kun ji cewa dan majalisar dattawan Najeriya mai wakiltan mazabar Kano ta kudu, Sanata Kabiru Gaya, ya yi rashin daya daga cikin 'yayansa.

Kara karanta wannan

Yan Ta'addan ISWAP Sun Yi Jana'izarsa Mambobinsu 26 Da Soji Suka Kashe

'Dan masu suna Sadiya Kabiru Gaya, ya rasu ne ranar Talata 13 ga Satumba kuma an yi jana'izarsa da yamma bayan Sallar La'asar a birnin tarayya Abuja.

Marigayin ya kasance Lauya da hukumar manajin dukiyoyi watau AMCON da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel