Yan Ɗarikar Tijjaniyya ba za su yi sak ba a 2019 –Dakta Muhammad Tahar

Yan Ɗarikar Tijjaniyya ba za su yi sak ba a 2019 –Dakta Muhammad Tahar

Rahotanni sun kawo cewa kungiyar mabiya darikar Tijanniya sun sha alwashin cewa bazasu sake yin zaben sak a shekarar 2019 ba sai sun tabbatar da wanda zaiyi dasu bayan a gwamnati.

Shugaban kungiyar Gausiyya na kasa baki daya wato Gausiyya Islamic Moɓerment in Nigeria, Dakta Muhammad Tahar Adamu ne ya sanar da hakan a wajen taron mauludin Shehu Ahmadu Tijjani da suka gudanar a rufaffen ɗakin wasa na sani Abacha dake ƙofar Mata.

A yayin jawabinsa lokacin taron, Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yaba da samar da wannan kungiyar da Dakta Muhammad Tahar ya yi tare da basu tabbaci cewa yana tare da manufofin kungiyar ta ɗarikar Tijjaniyya.

Gwamna Ganduje ya ce, ko a baya da aka samu wasu suka fake da ɗarikar suna abin da bai kamata ba, gwamnatin Kano ta sa an kama su, an kai su ga sharia har aka yi musu hukuncin kisa, wanda ba a zartas ba saboda shari’ar ta fi ƙarfin hukuncin gwamnatin Kano.

Ya yi nuni da cewa ko yanzu a wannan gwamnati tasa, lamba Biyu a Kano, wato mataimakin gwamna, Farfesa Hafizu Abubakar ɗan Tijjaniyya ne.

Yan Ɗarikar Tijjaniyya ba za su yi sak ba a 2019 –Dakta Muhammad Tahar
Yan Ɗarikar Tijjaniyya ba za su yi sak ba a 2019 –Dakta Muhammad Tahar

Da yake nasa jawabin Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sunusi II ya ja hankalin ‘yan ɗarika da cewa, shari’a ba ta yarda mutum ya tsaya saboda ɗarika ba ya sana’ar komai ba. Allah ya yi umurni da a bazu a bayan ƙasa a nemi arziki.

Sarkin Kano ya umurci Musulmi su haɗa kansu akan abin da yake alheri na tsoron Allah ba akan son zuciya ba, wannan shi ne koyarwar ɗarikar Tijjaniyya.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya goyi bayan shirin El-Rufai na koran malamai 22,000 a Kaduna

Shugaban kungiyar, Dakta Muhammah Tahar ya ci gaba da cewa; ba zai yiwu ana tuwo da garinsu ana sam musu a hannu ba. Domin su suka fi kowa yawa a ƙasar nan. “Kashi 55% ‘yan Tijjaniyya ne, idan haka ne ya za a yi shugaban ƙasa ko Gwamna ko ‘yan majalisa ba za a yi dasu ba?” inji shi.

Dakta Baba Imposibble ya ƙara da jaddda cewa daga yanzu ba za su yarda ba,duk wani wanda zai kafa Gwamnati sai dasu a cikinta,daga gwamna har shugaban ƙasa sun shata layi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng