Peter Obi Ya Yi Wa Shugaba Tinubu Sabon Shagube Kan Bayanan Karatunsa a Jami'ar Chicago

Peter Obi Ya Yi Wa Shugaba Tinubu Sabon Shagube Kan Bayanan Karatunsa a Jami'ar Chicago

  • Peter Obi, ɗan takarar jam'iyyar Labour a zaben shugaban ƙasa na 2023, ya soki Shugaba Tinubu kan ƙoƙarin hana a bayyana takardun karatunsa na jami'ar jihar Chicago
  • A cikin wani faifan bidiyo da Reno Omokri, tsohon hadimin shugaban ƙasa Jonathan ya sanya, an nuna Obi yana cewa za a iya tantance bayanan karatunsa ta yanar gizo
  • A cikin faifan bidiyon, Obi ya ce idan wani ɗan Najeriya ya ziyarci NSUKKA domin samun bayanan karatunsa, jami'ar za ta ba shi kwafinsa

An ga Peter Obi, ɗan takarar jam'iyyar Labour Party (LP) a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi na ranar 25 ga watan Fabrairu, yana yin tsokaci game da bayanan takardun karatun Shugaba Bola Tinubu na jami'ar jihar Chicago (CSU).

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Reno Omokri, wanda tsohon hadimin Goodluck Jonathan ne, ya sanya wani bidiyo na tsohon gwamnan yana magana kan bayanan karatunsa.

Kara karanta wannan

Abdullahi Adamu Ya Bayyana Wani Muhimmin Abu 1 Da Tinubu Ya Gaya Masa Bayan Ya Yi Murabus Daga Shugabancin APC

Peter Obi ya yi wa Tinubu shagube
Peter Obi ya yi wa Tinubu shagube kan kokarin hana bayyana takardun bayanan karatunsa a jami'ar CSU Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Peter Obi
Asali: Twitter

A cikin bidiyon, Obi ya bayyana yadda bayanan karatunsa za su iya samuwa ga ɗaukacin ƴan Najeriya, inda ya ƙara da cewa jami'ar da ya yi, na iya bayar da kwafin shaidar karatunsa.

Abin da Peter Obi ya ce game da bayanan takardun karatun Tinubu

A cikin bidiyon, Obi ya bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sunana Peter Obi, ni ɗan garin nan ne, na yi karatu a wannan makarantar firamare, wannan makarantar sakandare, wannan jami'a."

An ji sautin dariyar mutanen da ke sauraronsa, inda ya cigaba da cewa:

"Bana buƙatar sanya umarnin kada a gani, ka je Nsukka ka gaya musu, za su baka kwafinsa."

Martanin ƴan Najeriya kan kalaman Peter Obi

Wasu ƴan Najeriya sun garzaya sashen sharhi don mayar da martani kan bidiyon. Ga kaɗan daga ciki a nan ƙasa:

@sunnshyn01 ya rubuta:

"A yi haƙuri, amma ban ga wani izgili a nan ba, abin da kawai na ke gani shi ne an isar da saƙo."

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Kungiyar Manyan Ma'aikatan Jami'o'in Najeriya Ta Yi Babban Rashi

Amaka Agbara ta rubuta:

"Don Allah, ina izgili a nan? Mutumin da kawai ya zo ya faɗi gaskiya."

Oyela ya rubuta:

"Na gode wa Allah da ya sanya saboda Tinubu, muka fahimci cewa ilimi yaudara ne da ɓata lokaci a Najeriya kafin ka riƙe muƙamin gwamnati. Wannan ba yana nufin sai ka zama ɗan Najeriya kafin ka zama shugaban Najeriya ba."

Kotu Ta Umarci a Saki Takardun Karatun Tinubu

A wani labarin kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi nasara kan Shugaba Tinubu a kotun Amurka.

Kotun yanki a jihar Illinois ta ba jami'ar jihar Chicago umarnin sakin bayanan takardun karatun Shugaba Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel