Guru Maharaji ya bukaci Buhari ya nada shi a matsayin mai bashi shawara domin ya jagoranci ma’aikatar man fetur da sauransu

Guru Maharaji ya bukaci Buhari ya nada shi a matsayin mai bashi shawara domin ya jagoranci ma’aikatar man fetur da sauransu

Babban matsafi nan kuma Shugaban gidauniyar One Love Family, Sat Guru Maharaj ji, a ranar Talata, 4 ga watan Yuni yayi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nada shi a matsayin mai bashi shawara na tsarkin jiki.

Yace akwai bukatar hakan saboda sauran kungiyoyin addini da shuabanninsu sun gaza.

Maharaj ji ya gabatar da wannan bukata ne a lokacin wani taron manema labarai.

An gudanar da taron ne a kauyen Maharaj ji da ke hanyar babbar tikin Lagos/Ibadan.

Yace daga cikin abubuwan da ya ke sanya rai shine Shugaban kasar ya nada sa a matsayin wanda zai jagoranci ma’aikatun ruwa, noma, mai da gas a mulkin Buhari na biyu.

Baya ga neman a bashi mukami, matsafin ya kuma yi magana kan sauran lamura.

Yace gwamnatin tarayya na bukatar kara albashi sannan ta inganta jin dadin alkalai a kasar domin hana su karban cin hanci kai tsaye ko ta hannun wakilai.

KU KARANTA KUMA: Allah ya yiwa tsohon kwamishinan Kaduna, Abdulsalam Baba Ahmed rasuwa

Ya kuma yi kira ga samar da yan sandan jiha, cewa zai taimaka sosai wajen inganta lamarin tsaro a kasar.

Maharaj ji ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta bayyana sunayen wadanda ke da hannu a almubazaranci da kudaden wasu kamfanonin da aka siyar a Najeriya, ciki harda na jiragen saman Najeriya, Ajaokuta Steel, Delta Steel, hukumar NEPA da saurasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng