DCD Ta Gano Makarkashiyar da Ahmad Lawan Suke Shiryawa Kafin Zaben Majalisa

DCD Ta Gano Makarkashiyar da Ahmad Lawan Suke Shiryawa Kafin Zaben Majalisa

  • Kungiyar DCD ta kira taron manema labarai, ta shaida cewa ana kokarin canza dokokin majalisa
  • Shugaban kungiyar ya ce shugabannin majalisa masu barin gado za su birkita al’adar zaben shugabanni
  • A cewar Aliyu Abdullahi, an kama hanyar kawo wani sabon shiga ya gaji kujerar Ahmad Lawan

Abuja - Wata kungiya mai suna DCD mai ikirarin kare damukaradiyya a Najeriya ta zargi Ahmad Lawan da Ovie Omo-Agege da neman canza dokar majalisa.

A rahoton This Day, an ji kungiyar DCD ta na zargin shugaban majalisa da mataimakinsa da kokarin yin garambawul a dokar shiga zaben majalisa.

Idan zargin ya tabbata, Sanata Ahmad Lawan zai bada dama ga sababbin shiga majalisa su dare kujera, akasin tsohuwar al’adar da aka saba da ita a kasar.

Shugaban DCD, Alhaji Aliyu Abdullahi ya fitar da jawabi a garin Abuja inda aka ji yana gargadin hakan ya ci karo da kundin tsarin mulki da damukaradiyya.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Samu Goyon Bayan Na Kusa da Shugaba Buhari a Zaben Majalisa

Za a kawo 'dan amshin-shata

Aliyu Abdullahi yake cewa Lawan da Sanata Ovie Omo-Agege su na so su kakaba yaronsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dr. Ahmad Lawan
Shugaban Majalisa, Dr. Ahmad Lawan Hoto: @DrAhmadLawan
Asali: Twitter

"Mu na so mu sanar da zababbun Sanatoci da daukacin ‘Yan Najeriya mun gano aika-aikar shugaban majalisa, Ahmad Lawan da mataimakinsa, Ovie Omo-Agege.
Su na so su canza dokoki da tsarin da suka ce sai wanda ya dade a majalisa zai samu mukami.
Mu na da labari mai karfi cewa Lawan and Omo-Agege su na kutun-kutun domin su kakaba 'dan amshin-shatansu a matsayin shugaban majalisar tarayya ta goma.
Abin mamaki shugaban majalisa da mataimakinsa za su yi wannan alhali akwai Sanatan da ya dace wanda shugaba mai jiran gado ya gamsu ya yi aiki da shi.

Za a iya zuwa kotu

A rahoton Sun, Aliyu Abdullahi ya ce yin hakan zai saba sashe na 311 na kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Buhari Zai Shilla Ingila Don Halartar Nadin Sarautar Sarki Charles

A matsayinsu na masu kare kundin tsarin mulki, DCD sun fara haramar kai kara a kotun tarayya, za su kalubalanci canza dokokin majalisar tarayya kafin zabe.

Ana yakar APC a majalisa

Hon. Fred Agbedi, Hon. Nicholas Mutu, Hon. Wole Oke, Hon. Beni Lar da Hon. Kingsley Chinda sun jagoranci ‘yan adawa wajen yakar APC a majalisa.

Rahoto ya nuna makasudin zaman da suke yi shi ne shugabannin majalisa su fito daga jam’iyyun adawa irinsu PDP, LP ko NNPP a maimakon APC mai-ci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel