Titin Abuja zuwa Kano: Shugaba Tinubu Ya Tsara Kunyata Buhari cikin Watanni 14
- Ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idris, ya tabbatar da cewa aikin titin Abuja zuwa Kano zai kammala cikin watanni 14 domin amfanin jama'a
- An kasa aikin titin zuwa gida uku domin samun sauƙin gamawa kuma gwamnatin tarayya ta canza ɗan kwangila
- Ministan ayyuka, David Umahi ya bayyana cewa an ƙara faɗaɗa aikin har zuwa filin jirgin sama na Aminu Kano da kuma titin Abuja zuwa Lokoja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin jagoranci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta ce za a kammala aikin gina titin Abuja-Kaduna-Kano nan da watanni 14.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan, ya ce an gama shirin fara aiki da titin nan da shekara guda da wata biyu.

Asali: Twitter
Ya bayyana hakan ne yayin bikin kaddamar da gyaran sashen farko na hanyar daga Abuja zuwa Kaduna, wanda aka gudanar ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Bola Tinubu ta kasa aikin gida 3
Sashen farko na hanyar ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna, na biyu daga Kaduna zuwa Zaria, sannan na uku daga Zaria zuwa Kano.
Ayyukan da aka tsara sun haɗa da ɓanɓare titin da sake gyara shi, cike gibin gefen titin, samar da duwatsu domin kafa tushe mai ƙarfi da shinfiɗa sabon titi
Sauran ayyukan sun haɗa da gina magudanan ruwa a tsakiya da gefe, sanya bangon da zai raba hanyar zuwa da ta dawowa a tsakiya da dai sauransu.
Muhammed Idris ya ce ministan ayyuka, Mr. David Umahi, ya yi cikakken bayani kan hanyar, ya kuma kawo ƙarshen batun siyasa da aka sa wanda ya hana aikin ci gaba.
Tinubu ya shirya ƙarasa titin da Buhari ya fara

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
“Shugaba Bola Tinubu ya himmatu wajen ganin cewa an kammala wannan hanya daga Abuja zuwa Kano cikin wata 14.
"Wannan shi ne dalilin da ya sa gwamnati ta soke tare da ƙwace aikin daga hannun tsohon ɗan kwangilar wanda ya ce zai kammala aikin cikin shekara uku, amma gwamnati ta ƙi amincewa da hakan.
“Hakan ne ma ya sa aka kasa aiki kashi uku domin samun saiƙi, ‘yan Najeriya musamman masu bin wannan hanya sun kosa su ga an kammala aikin. Za mu yi sabuwar hanya nan da watanni 14," in ji Idris.
Gwamnatin Tarayya ta faɗaɗa aikin titin
A nasa jawabin, ministan ayyuka, David Umahi ya ce an faɗaɗa aikin titin har zuwa filin jirgin sama na Aminu Kano da kuma hanyar Abuja-Lokoja mai nisan kilomita biyar.
Umahi ya tabbatar da cewa titin zai sami fitilu na hasken rana kuma zai iya ɗaukar shekaru 50 zuwa 100.
Ya ce akwai umarnin kai-tsaye daga Shugaban Kasa don tabbatar da cewa babu wani jinkiri da za a sake samu har zuwa lokacin da za a kammala aikin.
Minista zai kashe N8bn a 2025
A wani labarin, kun ji cewa ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce ma'aikatarsa za ta kashe Naura biliyan 8 wajen wayar da kan ƴan Najeriya a 2025.
A cewarsa, an shirya wayar da kan jama'a ne don rage satar kayan wuta da kuma biyan kuɗin wutar a lokacin da ya dace.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng