Matasan Arewa Sun Yi Magana kan Goyon Bayan Shugaba Tinubu a Zaɓen 2027
- Matasan Arewa sun bayyana cewa har yanzun ba a kai ga cimma matsaya kan marawa Tinubu baya ya yi tazarce ko akasin haka ba a 2027
- Shugaban ƙungiyar matasan (AYCF), Yerima Shettima ya ce duk wanda ya ce Arewa ta ɗauri ɗamarar yaƙar Bola Tinubu ƙarya yake
- Ya ce za su duba kokarin shugaban ƙasa a zangon farko kafin yanke shawarar goyon bayansa ko juya masa baya a zaɓe na gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Shugaban ƙungiyar matasan Arewa (AYCF), Yerim Shettima ya ce har yanzu ba su yanke shawara kan ko za su goyi bayan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a 2027 ba.
Idan baku manta ba dakatacccen shugaban kungiyar tuntuɓa ta Arewa watau ACF, Mamman Osuman, ya ce ƴan Arewa ba za su sake zaɓen Tinubu ba.
A cewarsa, Arewa za ta jingine shugaban kasa, Bola Tinuuɓa 2027, ta marawa ɗan Arewa baya domin ceto yankin da Najeriya daga halin ƙuncin rayuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Arewa za ta goyi bayan Bola Tinubu a 2027?
A wata hira da jaridar Punch, shugaban matasan Arewa ya ce har yanzu ba su yanke shawara ba, suna kan teburin tattaunawa kan wanda za su zaɓa a 2027.
Yerima Shettima ya yi nuni da cewa Arewa na da ƙarfin siyasa kuma za su kalli ayyukan Tinubu a zangon farko kafin yanke goyon bayansa ko yaƙarsa a 2027.
Ya ce waɗanda ba su jin daɗin mulkin Bola Tinubu suna da ƴancin bayyana fushinsu da kokensu, amma duk da haka Arewa ba za ta yi gaggawar ɗaukar mataki ba.
Ƴan Arewa ba zasu zaɓi Tinubu a 2027 ba?
"Har yanzu Arewa ba ta kai ga daukar matsaya ɗaya kan Tinubu ba, amma wadanda ba su gamsu da gwamnatinsa ba suna da damar nuna fushinsu a kansa.
"A yanzu dai Arewa ba ta yanke shawara kan goyon bayan Tinubu ko akasin haka ba, amma mutanenmu na son ya sauya wasu tsare-tsarensa, ya fito da manufofin da za su sa murmushi a fuskokin ƴan Najeriya."
"Don haka duk wanda ya faɗa mana Arewa ta ɗaura ɗamar yaƙar Tinubu karya yake, har yanzu ba mu ɗauki matsaya ba kuma ba na tunanin za mu yanke shawara nan kusa."
- Yerima Shettima.
Wani matashin ɗan siyasa a Katsina, Yusuf Abdul ya shaidawa Legit Hausa cewa sama da kaso 80% na ƴan Arewa ranar zaɓe kawai suke jira su sauke fushinsu.
Ya buƙaci Shugaba Tinubu ya sake nazari kan wasu tsare-tsarensa idan har yana son tazarce a zaɓen 2027.
"Mutane suna cikin wahala kuma duk shugaban ƙasa ake ɗora ma laifin, yanzu ga wannan batun na haraji, ba zan ce babu masu goyon bayan Tinubu ba amma ƴan kaɗan ne.
"Sai dai kuma ka san mutanen mu da son abin duniya, a ranar zaɓe za a iya canza masu ra'ayi da kuɗi ƴan kaɗan, Allah dai ya zaɓa mana mafi alheri.
Jam'iyyu sun fara yiwa Tinubu taron dangi
Kuna da labarin cewa takarar Bola Tinubu a zaben 2027 na cigaba da fuskantar matsaloli daga jam'iyyun adawa da kuma sauran kungiyoyi
Jam'iyyun adawa da dama sun shirya yin wata irin haɗaka mai ƙarfi domin tunkarar zaben da kifar da shugaban kasa Tinubu
Asali: Legit.ng