Kotu: Ana Shirin Hana Majalisa Tantance Garo a matsayin Mataimakin Gwamnan Kano
- Wasu lauyoyin sun shigar da ƙara a kotu don hana tantance Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kano
- Haka kuma sun rubuta wasika ga Majalisar dokokin Kano ta dakatar da duk wani shiri a kan batun tantance Garo har sai kotu ta yanke hukunci
- Rikicin siyasa da neman goyon baya na ƙara ƙamari a cikin jam’iyyar APC a Kano game da wanda zai zama mataimakin Abba Kabir Yusuf
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wani sabon rikicin shari’a ya ɓarke kan batun cike gurbin mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamred Aminu AbdusSalam Gwarzo.
Wasu lauyoyi sun rubuta wasika inda suka bukaci Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da duk wani yunkuri na tantance Murtala Sule Garo har sai an kammala shari’ar da ke gaban kotu.

Source: Facebook
Daily Nigerian ta wallafa cewa wannan bukata na kunshe ne cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 15 ga Afrilu, 2026, da lauyoyi Suleiman Mohammed & Co. suka aikewa da kakakin majalisar, Jibrin Falgore.
Ana son hana tantance Murtala Sule Garo
Rahoton ya ce lauyoyin suna wakiltar Kuliyya Muhammad Salihu da wasu mutum biyu da suka shigar da kara kan lamarin tantance Garo a matsayin mataimakin gwamnan Kano.
A cewar lauyoyin, sun riga sun kai ƙara gaban babbar kotun jihar Kano, inda suka kalubalanci yunkurin tantance Garo a matsayin mataimakin gwamna.
Sun bayyana cewa tunda shari’ar tana gaban kotu mai iko, to lamarin ya zama “sub judice”, wato bai dace a ci gaba da daukar wani mataki ba har sai an yanke hukunci.
Shari’ar, mai lamba K/360/2026, na nan tana jiran sauraro a babbar kotun jihar. Lauyoyin sun kuma gargadi majalisar da ta guji duk wani mataki da zai iya kawo cikas ga tsarin shari’a ko nuna son rai yayin da kotu ke duba batun.

Kara karanta wannan
Kudurin hana Trump sayar wa Isra'ila bama bamai ya gamu da cikas a majalisar dattawa
Siyasar jihar Kano za ta dauki zafi
Kafin wannan sabon rikici, an riga an shiga yanayin takun-saka a siyasar Kano kan wanda zai zama mataimakin gwamna Abba Kabir Yusuf.

Source: Facebook
Rahotanni sun nuna cewa bangarorin Ganduje da na Barau na jam’iyyar APC sun zabi mutane uku da suka hada da Murtala Garo, tsohon kakakin majalisa Kabiru Rurum, da kuma Rabiu Bichi.
Duk da haka, har yanzu gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, bai aika wa majalisa sunan wanda zai zama mataimakin gwamna a hukumance ba.
Sai dai dukkannin masu neman mulkin suna ci gaba da neman goyon bayan ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki domin samun wannan matsayi.
Wannan na iya jinkirta yanke hukunci kan wanda zai maye gurbin mataimakin gwamna, tare da kara janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin bangarorin siyasa.
Gwamnatin Kano ta shiga shari'a da Garo
A baya, mun wallafa cewa Gwamnatin jihar Kano ta sake shigar da ƙara a kotun ɗaukaka ƙara game da tsohon kwamishina Murtala Sule Garo da wasu mutane.
Matakin shigar da ƙarar ya zo ne watanni tara bayan kotun ta yanke hukunci, a daidai lokacin da ake matsin lamba kan gwamna ya naɗa Garo mataimakinsa.
Takardun shari’a sun nuna gwamnati na ƙalubalantar hukuncin gaba ɗaya, inda ake zargin Murtala Suke Garo ya karkatar da biliyoyin kuɗin kananan hukumomi.
Asali: Legit.ng

