Shugaban kasa A 2023: Buhari Bai Damu Da Takarar Tinubu Ba, Inji Baba-Ahmed

Shugaban kasa A 2023: Buhari Bai Damu Da Takarar Tinubu Ba, Inji Baba-Ahmed

  • Gabannin babban zaben 2023, abokin takarar Peter Obi na jam'iyyar LP, Datti Baba-Ahmed ya ce takarar Bola Tinubu na APC ba komai bane a wajen Shugaba Muhammadu Buhari
  • Baba-Ahmed ya ce Tinubu ne ya gina Buhari har ya kai ga zama shugaban kasa amma akasin haka ne zai faru a yanzu da tsohon gwamnan na Lagas ke son ya gaje shi a 2023
  • Ya ce a yanzu jam'iyya daya tilo da tayi saura a kasar nan ita ce Labour Party domin APC da PDP sun shide

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Datti Baba-Ahmed, ya bayyana cewa takarar shugabancin Asiwaju Bola Tinubu na APC, ba komai bane a wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Baba-Ahmed ya fadi hakan ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba, yayin da ya bayyana a shirin Sunday Politics na gidan talbijin din Channels.

Kara karanta wannan

2023: Baba-Ahmed Ya Fasa Kwai, Ya Fadi Yan Takarar Shugaban Kasa 2 da Ba Zasu Iya Kashe Kudin da Suka Tara Ba

Baba-Ahmed, Tinubu da Buhari
Shugaban kasa A 2023: Buhari Bai Damu Da Takarar Tinubu Ba, Inji Baba-Ahmed Hoto: Sen. Datti Baba-Ahmed PhD, Buhari Sallau
Asali: Facebook

A cewarsa, Buhari ya gama da Najeriya kuma zai 'bata Tinubu bayan dukkanin nasarorin da ya samu a siyasarsa.'

Baba-Ahmed ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"A taron majalisar dinkin duniya, shi (Buhari) ya ce abu guda da zai bari shine zabe na gaskiya. Yanzu, wannan ya karya zuciyar APC.
"Wa ya gina Buhari bayan Allah madaukakin sarki? Tinubu. Duk yunkurin Buhari ya gaza, Tinubu ya zo sannan ya kara miliyoyin kuri'u ya gina Buhari.
"Wa zai lalata shirin Tinubu bayan duk nasarorin siyasarsa? Buhari, saboda Buhari ya gama shekarunsa takwas. Ba batun ya aka tafiyar da mulkin Najeriya bane, sun gama da Najeriya, sun gama da kowa. Tinubu na iya tarwatsewa, hakan baya nufin wani abu ga Buhari kuma haka Buhari yake."

PDP da APC sun shafe Najeriya, Labour Party ce jam'iyyar da tayi saura

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Ja Wa Kansa, Wani Babban Jigon APC Ya Fice Daga Jam'iyyar

Baba-Ahmed ya kuma ce ya rushe duk wasu shinge da aka gina a kan hanyar Obi a arewa, yana mai cewa tsohon gwamnan na jihar Anambra ya samu karbuwa sosai yanzu a wajen matasa da sauran mutanen yankin wanda ya kara karfafa shi a zaben mai zuwa.

A cewarsa, APC da PDP sun zama tamkar tarihi ne kuma jam'iyya daya da yayi saura a kasar nan a yanzu ita ce Labour Party.

Yan takarar APC na shafawa Peter Obi bakin fenti a idon arewa

A wani labarin kuma, Datti Baba-Ahmed ya zargi yan takarar jam'iyyar APC mai mulki da amfani da duk wata dama da ta zo masu wajen bata Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a wajen yan arewa da Musulmai.

Baba-Ahmed ya ce sabanin abun da ake son dirsawa a zukatan mutanen arewa, Obi na matukar kaunar al'ummar yankin cewa wannan ne babban dalilin da yasa ya zabe shi a tafiyar shi a 2023.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Abokin Takarar Peter Obi Ya Yi Garumin Zargi A Kan Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel